An Budewa Sarki Wuta da Bindiga bayan Sace Shi a Kaduna, an Yasar da Gawarsa

An Budewa Sarki Wuta da Bindiga bayan Sace Shi a Kaduna, an Yasar da Gawarsa

  • An tsinci gawar Hakimin Dutsan Gaya, Mai Tala Ariga Makama, bayan wasu da ake zargin ‘yan banga ne suka yi garkuwa da shi
  • An gano gawar basaraken a gefen garin Sabon Garin Rimau da ke karamar hukumar Kajuru, Jihar Kaduna, dauke da raunukan harbin bindiga
  • Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa an fara bincike domin gano musabbabin kisan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Wani lamari mai tayar da hankula ya auku a Kajuru a Jihar Kaduna, inda aka tsinci gawar Hakimin Dutsan Gaya, Mai Tala Ariga Makama bayan an yi awon gaba da shi.

Rahotanni sun nuna cewa basaraken ya rasa ransa ne bayan wasu da ake zargin 'yan sa-kai ne sun dauke shi da safiyar Lahadi, daga bisani aka gano gawarsa dauke da raunukan bindiga.

Kara karanta wannan

Sojoji, 'yan sanda da 'yan banga sun hadu sun gwabza artabu da 'yan bindiga

Kaduna
An kashe basarake a jihar Kaduna. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Mai sharhi kan lamuran tsaro, Zagazola Makama ya wallafa bayanin da 'yan sanda suka yi kan lamarin a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta ce an tsinci gawar hakimin ne a yankin Sabon Garin Rimau, kuma a halin yanzu ana bincike domin gano musabbabin kisan da aka masa.

Yadda aka kashe basarake a Kaduna

Wata majiyar ‘yan sanda ta bayyana cewa wasu da ake zargin ‘yan banga ne sun kutsa cikin garin Dutsan Gaya da safiyar Lahadi, inda suka yi awon gaba da hakimin.

'Yan sanda sun bayyana cewa:

“An sace shi ne da sassafe, daga bisani aka tsinci gawarsa a gefen garin Sabon Garin Rimau dauke da raunukan harbin bindiga,”

Bayan samun rahoton kisan, DPO na yankin Kasuwan Magani ya jagoranci tawagar ‘yan sanda da jami’an tsaro zuwa wurin da aka tsinci gawar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an dauki gawar basaraken zuwa asibitin garin, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa sakamakon harbin bindiga.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta sanar da fara daukan 'yan sanda a karon farko a 2025

Rundunar ‘yan sanda ta fara bincike

Bayan da lamarin ya faru, rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta gudanar da taron gaggawa da shugabannin al’umma da matasan yankin domin kwantar da hankalin jama’a.

Bugu da kari, jami’an tsaro sun yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da ba su goyon baya wajen bankado wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Yan sanda
Sufeton 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

A halin yanzu, an ajiye gawar basaraken a asibitin Gomna Anwan da ke Kakuri, inda za a gudanar da binciken asibiti domin gano hakikanin abin da ya janyo mutuwarsa.

Jama’a sun bukaci a yi adalci

Mutanen yankin Dutsan Gaya sun bayyana matukar bakin cikinsu game da wannan mummunan kisa, inda suka bukaci hukumomi da su gaggauta daukar matakin adalci.

Wasu dattawan yankin sun yi kira ga gwamnati da ta dauki tsauraran matakan tsaro domin hana irin wannan ta’asa faruwa a gaba.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dakile shirin masu garkuwa da mutane, sun cafke miyagun masu laifi

A halin yanzu dai, ana ci gaba da zaman dar-dar a yankin, yayin da hukumomi ke ci gaba da bincike domin gano hakikanin wadanda ke da hannu a kisan basaraken.

Sojoji sun ceto mutane a jihar Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya hade da 'yan sanda da 'yan bindiga sun ceto mutanen da aka sace a jihar Katsina.

Jami'an tsaron sun kai farmaki ne kan 'yan bindigar bayan sun sace mutane da dabbobi a wasu 'yankuna na jihar a lokacin da suka fito fashi da makami.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng