Martanin Jiga Jigan Siyasar Najeriya kan Abin da Littafin IBB Ke Kunshe da Shi

Martanin Jiga Jigan Siyasar Najeriya kan Abin da Littafin IBB Ke Kunshe da Shi

FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙasan Najeriya a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya ƙaddamar da littafi kan tarihin rayuwarsa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Janar IBB kamar yadda ya fi shahara, ya ƙaddamar da littafin ne shekara 32 bayan barinsa kan kujerar mulkin Najeriya.

Tinubu ya yabi Janar IBB
Tinubu na daga cikin wadanda suka yi magana.kan littafin Janar IBB Hoto: @DOlusegun, @ShehuSani
Asali: Twitter

Me Littafin rayuwar IBB ya ƙunsa

A cikin littafin dai, Janar IBB ya yi magana kan batutuwa da dama da suka shafi rayuwarsa da kuma mulkin da ya yi a ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Littafin ya dauko tarihi tun daga zuwan kakan Babangida kasar Neja da kuma auren mahaifiyarsa zuwa yadda ya taso a shekarun 1940.

Tsohon shugaban ƙasan ya kuma amince cewa Moshood Abiola ne ya lashe zaɓen ranar, 12 ga watan Yunin 1993, wanda ya soke.

Attajirai sun ba Janar IBB gudunmawa

Jaridar TheCable ta rahoto cewa manyan attajiran Najeriya sun ba da gudunmawar kuɗi, domin gina katafaren ɗakin karatu na Janar IBB a wajen taron.

Kara karanta wannan

"Mun raba gari," El-Rufa'i ya fadi abin da ya kashe abotarsa da Uba Sani, Ribadu

Aliko Dangote ya ba da gudunmawar N8bn da za a riƙa ba da N2bn duk shekara har na tsawon shekara huɗu.

Attajirin na Afrika ya kuma yi alƙwarin idan aikin ya wuce wannan lokacin, zai riƙa ba da N2bn duk shekara har sai an kammala shi.

Abdulsamad Rabiu mai kamfanin BUA ya ba da N5bn, yayin da Theophilus Danjuma ya ba da N3bn.

Sanannen ɗan kasuwa, Arthur Eze ya ba da N500m, Sanata Sani Musa (Neja ta Arewa) ya ba da N250m, yayin da Mustafa Chike-Obi na bankin Fidelity ya ba da N100m.

Me ƴan siyasa suka ce kan littafin Janar IBB?

Ƴan siyasa da dama sun tofa albarkacin bakinsu kan littafin na Janar IBB, inda wasu riƙa yaba masa kan abubuwan da ya faɗa a cikinsa.

Wasu kuwa sun caccake shi, inda suka nuna cewa littafin cike yake da ƙarya da ƙarairayi.

Ga wasu daga cikin waɗanda suka yi magana:

Kara karanta wannan

Dakatar da ƴan Majalisa 4 a Kano ya tayar da ƙura, sun yi wa Kwankwaso rubdugu

1. Bola Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu halartar bikin ƙaddamar da littafin wanda aka gudanar a birnin tarayya Abuja.

A wata sanarwa a shafin statehouse.gov.ng, mai girma Bola Tinubu ya yabawa tsohon shugaban kan bayyanawa duniya cewa MKO Abiola ne ya lashe zaɓen ranar, 12 ga watan Yunin 1993.

Tinubu ya bayyana cewa Janar IBB ya nuna tsantsar ƙwarin gwiwa da kishin ƙasa ta hanyar bayyana cewa MKO Abiola ne ya lashe zaɓen.

Shugaban kasar bai karanta littafin ba, amma ya sha alwashin zai yi hakan.

Na yi farin ciki dangane da abin da ka ce kan zaɓen ranar 12 ga Yuni. Mai girma Janar ba za mu manta ba wajen ci gaba da yi maka addu'a. Na saurareka da kyau."
"Ina yi maka godiya kan komai, kan yadda kake, kan abin da ka yi da yadda ka ba da gudunmawa wajen tarihin wannan ƙasar mai girma."

Kara karanta wannan

Malam El Rufai ya bayyana wanda yake so ya karɓi mulki daga hannun Tinubu a 2027

- Bola Ahmed Tinubu

2. Shehu Sani

Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani na daga cikin mutanen da tofa albarkacin bakinsu kan littafin na Janar IBB.

A wani rubutu da ya yi a shafinsa na X, Shehu Sani ya yabawa Janar IBB kan bayyana cewa MKO Abiola ne ya lashe zaɓen ranar, 12 ga watan Yunin 1993.

Sai dai, ya nuna takaicinsa kan cewa ƴan gwagwarmayar da suka yi ta faɗi tashi kan ganin an tabbatar da zaɓen sun riga mu gidan gaskiya.

3. Chidi Odinkalu

Chidi Odinkalu ya caccaki Janar IBB kan abubuwan da rubuta a cikin littafinsa wanda ya ƙaddamar.

A wani rubutu a shafinsa na X, Chidi Odinkalu ya zargi tsohon shugaban ƙasan da zama mutum mara nagarta kuma matsoraci, kan yadda ya riƙa ɗora alhakin wasu abubuwan da suka faru kan mutanen da suka riga da daɗewa da barin duniya.

Kara karanta wannan

Ni ba Ba-Yarbe bane: IBB ya fadi gaskiyar karin sunan 'Babangida' a cikin sunansa

"Littafin Ibrahim Babangida cike yake da zarge-zarge kan mutanen da suka riga da sun mutu. Ya jira har sai da suka mutu ta yadda babu wanda daga cikinsu zai tunkare shi. Hakan ya ƙara nuna shi a matsayin mutum mara nagarta."

- Chidi Odinkalu

Dalilin rashin ganin Buhari a taron littafin IBB

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani ƙusa a jam'iyyar APC a jihar Neja, Jonathan Vatsa, ya yi tsokaci kan rashin ganin Muhammadu Buhari a wajen ƙaddamar da littafin Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Jigon na APC ya bayyana cewa har yanzu tsohon shugaban ƙasan na jin zafin kifar da gwamnatinsa da Janar IBB ya yi a shekarar 1985.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng