Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Aika Saƙo ga Malamai Ana Shirin Fara Azumin Ramadan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Aika Saƙo ga Malamai Ana Shirin Fara Azumin Ramadan

  • Kungiyar jama'atu Nasrul Islam da ke karkashin jagorancin Mai alfarma Sarkin Musulmi ta buƙaci malamai su haɗa kansu
  • Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ce bai kamata sabanin fahimta ya rika jawo faɗa tsakanin musulmai ba
  • Sultan ya ja kunnen malamai su daina zagin juna musamman a wurin karatuttukansu yayin za a fara azumin Ramadan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Yayin da al’ummar Musulmi ke shirye-shiryen watan Ramadan, kungiyar Jama’atu Nasrul Islam (JNI) ta jaddada bukatar hadin kai da amana tsakanin malamai da shugabannin addini.

Shugaban JNI, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, ne ya bayyana hakan a taron da aka gudanar kan gabatowar Ramadan a Kaduna a ranar Litinin.

Sarkin Musulmi.
Kungiyar JNI ta bukaci malamai su haɗa kan Musulmi Hoto: Professor Isa Ali Pantami
Asali: Facebook

Ya kamata malamai su haɗa kansu

Punch ta tattaro cewa taken taron shi ne, “Kafofin sada zumunta da malaman addinin musulunci: Dalilan da ke kawo sabani tsakanin Malamai."

Kara karanta wannan

Gwamnan Sakkwato ya waiwayi malaman musulunci, an yi masu tanadin Ramadan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron ya mayar da hankali kan yadda ake amfani da kafafen sada zumunta wajen yada ilimi da kuma matsalolin da ke tasowa.

Da yake jawabi, Sultan ya bukaci al'ummar Musulmi da su kasance a inuwa ɗaya, su haɗa kansu tamkar tsintsiya maɗaurinki ɗaya.

"Dole ne mu hadu a inuwar Musulunci. Za mu iya samun sabanin fahimta kan abubuwa da dama, amma dole ne mu yi aiki tare domin ci gaban Musulunci."

Sarkin musulmi ya ba malamai shawara

Ya gargadi malamai da su guji zagin juna saboda sabanin fahimta, yana mai cewa kowa yana da ilimi, amma akwai wanda ya fi wani sani.

"Ya kamata mu ajiye saɓanin fahimtarmu, ka da mu bari irin haka ya raba kawunan Musulmi har ya kai ga zagin juna," in ji sarkin Musulmi.

Ya kuma bukaci malaman da su kiyaye ka’idojin Tafsiri don tabbatar da ingantaccen karantarwa a watan azumin Ramadan.

Mai alfarma sarkin Musulmi
Sultan ya buƙaci Musulmi su daina zagin juna kan sabanin fahimta Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Facebook

Malamai za su iya haɗa kan musulmai

Kara karanta wannan

Dakatar da ƴan Majalisa 4 a Kano ya tayar da ƙura, sun yi wa Kwankwaso rubdugu

A nasa jawabin, Sakataren JNI, Farfesa Khalid Aliyu, ya bayyana cewa malaman addini suna da rawar da za su taka wajen kawo hadin kai da fahimtar juna a tsakanin Musulmi.

Ya bukaci malamai da su guji bayar da fatawowi bisa ra’ayin kansu, yada tunanin da zai kawo rarrabuwar kai da makamantansu.

A cewarsa:

"Kafofin sada zumunta sun saukaka yadda malamai ke yada karatunsu, amma hakan ya kuma haifar da yada bayanan da ba su da tushe da kuma fatawowin da ke kawo rarrabuwar kai."

Khalid Aliyu ya ce JNI ta kafa dokoki na Tafsiri don hana malamai amfani da maganganun da ke da nasaba da bambancin akida.

Taron ya samu halartar manyan sarakuna da malamai daga sassan kasar nan, inda aka jaddada bukatar hadin kai da ci gaba.

Sultan ya ba ƴan Najeriya shawari

A wani labarin, kun ji cewa Sultan Muhammad Sa'ad III ya bukaci ƴan Najeriya da su rika kyautata junansu a wannan hali da ake ciki.

Kara karanta wannan

Limami: "Abin da ya kamata Musulmai su yi kafin a fara azumin watan Ramadan"

Sarkin musulmi ya bukaci masu hannu da shuni su rika tallafawa marasa galihu, sannan ya yi kira da masu ruwa da tsaki da su samar da zaman lafiya a tsakanin al'umma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262