Tinubu Ya Shigo da Motocin Noma domin Yaki da Yunwa da Samar da Abinci
- Gwamnatin tarayya ta sanar da shigo da rukunin farko na taraktoci 2,000 daga ƙasar Belarus don inganta noma a Najeriya
- Wannan shiri yana ƙarƙashin yarjejeniyar haɗin gwiwa da aka kulla tsakanin Najeriya da Belarus a watan Satumban 2024
- Za a raba taraktocin ta hanyoyi uku: sayarwa kai tsaye, haya ga manoma, da samar da cibiyoyin hidimar noma a fadin kasar nan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakin ƙara ƙarfafa aikin noma tare da inganta amfani da kayan zamani, yayin da rukunin farko na taraktoci 2,000 daga Belarus ya iso ƙasar nan.
Matakin na daga cikin matakan gwamnatinsShugaba Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da wadatar abinci da bunƙasa tattalin arzikin yankunan karkara.

Asali: Twitter
Ministan noma ya wallafa a X cewa an saukar da taraktocin a Kwali, Abuja, yayin da aka kammala shirin isar da wasu daga cikin su zuwa sassa daban-daban na ƙasar nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shirin haɗin gwiwar Najeriya da Belarus
Taron da aka gudanar a Kwali ya nuna irin yadda shirin haɗin gwiwar Najeriya da Belarus ke haɓaka aikin noma.
A cewar wani jami’in gwamnati, a halin yanzu an saukar da fiye da kwantena 200 masu ɗauke da taraktoci da kayan aikin noma a Lagos, inda wasu kwantena 20 ke kan hanyar zuwa Abuja.
Ministan noma, Sanata Abubakar Kyari ya ce:
“A yau kawai mun karɓi kwantena biyar, kowanne na ɗauke da taraktoci uku, wanda jimillar su ke zama 15 a wannan rukuni na farko.”
Ire-iren taraktocin da za a rabawa manoma
A cewar Sanata Kyari, shirin na bayar da taraktoci 2,000 tare da sauran kayan aiki 9,072 da za su taimaka wajen ayyukan noma daban-daban a Najeriya.

Kara karanta wannan
Mubarak Bala da ƴan Arewa 4 da aka taɓa yankewa hukuncin kisa kan ɓatanci ga Annabi

Asali: Facebook
Taraktocin sun kasu kashi huɗu dangane da ƙarfinsu da nau’ikan gonakin da za su dace da su:
- Taraktoci masu ƙarfin 90 (Masu taya biyu ) – guda 500
- Taraktoci masu ƙarfin 90 (Masu taya hudu ) – guda 500
- Taraktoci masu ƙarfin 80 (Masu taya biyu ) – guda 500
- Taraktoci masu ƙarfin 80 (Masu taya hudu ) – guda 500
Hanyoyin rabon taraktocin ga manoma
Domin tabbatar da cewa taraktocin sun kai ga manoma yadda ya kamata, gwamnati ta tsara hanyoyi uku na rabon su:
1. Sayarwa kai tsaye – Ga waɗanda ke son sayen taraktoci da kansu.
2. Shirin haya – Wanda zai bai wa manoma damar amfani da taraktoci ba tare da sayen su gaba ɗaya ba.
3. Cibiyoyin hidima – Za a kafa cibiyoyin da ke bayar da taraktoci domin haya ga ƙananan manoma.
An samu amfanin gona da dama a Neja
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Neja za ta fara fitar da kayan abinci daga Arewa zuwa kasashen ketare.
Gwamnatin Umaru Bago ta ce hakan na zuwa ne sakamakon kayan amfanin gona da suka samu a damunar da ta wuce saboda aiki da kayan noman zamai da suka yi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng