‘Ba Ku Biyan Haraji Sai Son Rayuwa Mai Inganci’: Akpabio Ya Dura kan Yan Najeriya
- Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yi magana game da biyan haraji a Najeriya inda ya ba da shawarwari
- Akpabio ya ce kasa da kashi 30% na 'yan Najeriya ne ke biyan haraji, amma kowa na bukatar abubuwan more rayuwa a kasar
- Ya goyi bayan gyaran dokokin haraji na Bola Tinubu, ya ce za su taimaka wajen inganta tattali da tabbatar da bin dokokin biyan haraji
- Ministan kudi, shugabannin haraji da wasu masana sun halarci taron don tattauna yadda dokokin haraji za su taimaki tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya koka game da kin biyan haraji da mafi yawan yan Najeriya ke yi.
Akpabio ya ce kasa da kashi 30% na 'yan Najeriya ne ke biyan haraji, duk da cewa kowa na bukatar ci gaban kasa.

Asali: Facebook
Akpabio ya koka game da rashin biyan haraji
Akpabio ya bayyana haka ne a lokacin da yake bude taron sauraron ra’ayin jama’a kan kudirin gyaran dokokin haraji da Bola Tinubu ya aike wa Majalisa, cewar Arise News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalaman Akpabio sun ta da kura inda kungiyar kwadago ta NLC da TUC da NECA suka caccake shi kan haka.
Vanguard ta ce kungiyoyin sun ce yan Najeriya na kin biyan haraji ne saboda gwamnatin ta gaza yin abin da ya dace gare su.
Sanata Akpabio ya ce dole ne a kawo sauyi, saboda ba za a ci gaba da yin abu daya ba tare da samun sakamako daban ba.
Ya tabbatar da cewa Majalisa za ta inganta aikin sa ido don tabbatar da cewa kudaden haraji suna tafiya ga abubuwan da za su amfanar da kasa.
Akpabio ya ce:
"Ban tunanin a yanzu bai wuce kashi 30% na 'yan kasa ne ke biyan haraji ba, amma kowa na bukatar ingantattun hanyoyi da sabis na zamani."

Sanata Akpabio ya magantu kan kudirin haraji
Akpabio ya ce sabbin dokokin haraji za su taimaka wajen tabbatar da cewa kowa yana biyan haraji cikin sauki, ba tare da la’akari da ra’ayin kowa ba.
An ji ya bukaci mutane su karanta kudirin dokokin harajin maimakon dogara ga labarai daga kafofin sada zumunta.
Ya kara da cewa:
"Wadannan dokoki ba kawai tattara haraji ba ne, suna da nufin bunkasa tattalin arziki da tabbatar da daidaito."
Wasu manyan jami’an gwamnati da masana sun halarci taron, ciki har da Ministan Kudi, Wale Edun, Shugaban Hukumar Haraji, Zacch Adedeji da Shugaban Hukumar Kwastam, Adewale Adeniyi.
Majalisa ta rikice kan wurin zaman Sanatoci
Mun ba ku labarin cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya fusata bayan Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta ki bin umarninsa.
Rikicin ya barke a majalisar yayin da aka matsar da kujerar Sanata Natasha amma ta ki amincewa da sabon wurin zama da aka ba ta.
Rikicin ya tsananta lokacin da jami’an tsaro suka kewaye Natasha domin fitar da ita daga zauren majalisa bayan gardama mai zafi ta barke.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng