'Don Allah Ka Bar Ni': Ribadu Ya Yi Martani ga El Rufai bayan Kalamansa kan Zaben 2031
- Mallam Nuhu Ribadu ya yi martani bayan kalaman tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai yayin hirarsa da 'yan jarida
- Ribadu ya ce ba zai yi ta gardama da Nasir El-Rufai ba, ya ce yana da abubuwan da suka fi muhimmanci fiye da jayayya da shi
- Ya jaddada cewa bai taɓa faɗa ko sukar El-Rufai a bainar jama’a ba, saboda girmamawa ga dangantakarsu da kuma iyalansu
- Ribadu ya musanta batun neman takarar shugaban kasa a 2031, ya ce duk hankalinsa na kan nasarar mulkin Bola Tinubu da ci gaban Najeriya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Mai ba shugaban ƙasa, Bola Tinubu shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu ya yi wa Nasir El-Rufai martani.
Ribadu ya ce ba shi da lokacin yin gardama ko jayayya da El-Rufai saboda lamuran mulki.

Source: Twitter
El-Rufai ya zargi Ribadu kan zaben 2031
Ribadu ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a yau Talata 25 ga watan Fabrairun 2025.
Martanin ya biyo bayan zargin da El-Rufai ya yi cewa Ribadu ya shirya neman kujerar shugaban kasa a shekarar 2031.
El-Rufai ya ce dalilin haka ne ma Ribadu ke neman taka duk wani da yake ganin zai zamo masa matsala a Arewacin Najeriya.
Tsohon shugaban EFCC ya ce akwai dangantaka mai ƙarfi tsakaninsu da kuma iyalansu wanda ba zai biye masa ba.
Ribadu ya fadi dangantarsa da Nasir El-Rufai
“Hankalina ya kai ga wata hira da Mallam Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan Kaduna, da aka yi da shi ranar Litinin da dare.
"Idan da ba don ka da a ce na yarda ba, da na yi shiru. Ina da abubuwan da suka fi muhimmanci fiye da shiga rigima da El-Rufai.
“Duk da ci gaba da ƙoƙarin tayar da hankali, ban taɓa faɗa ko sukar El-Rufai a bainar jama’a ba saboda girmamawa ga dangantakarmu da iyalanmu.
“Ina kira ga jama’a su yi watsi da kalaman El-Rufai a kaina, domin kaucewa rudani, ina tabbatarwa da kowa cewa ban taɓa tattaunawa da kowa kan takarar shugaban ƙasa a 2031 ba."

Source: Facebook
'Ba ni da lokaci a yanzu' - Ribadu ga El-Rufai
Ribadu ya ce a yanzu hankalinsa ya koma kan yadda za a samu ci gaba da kuma inganta rasuwar al'umma da Bola Tinubu ya sanya a gaba.
Ya kara da cewa:
“Dukkan hankalina na kan ci gaban Najeriya da kuma nasarar mulkin Shugaba Tinubu.
“Saboda haka, ina roƙon Nasir El-Rufai ya bar ni in mai da hankali kan aikina, kamar yadda ni ma ba na shiga harkokinsa.”
'Buhari ne sila' - El-Rufai kan takarar gwamna
A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi magana kan silar takararsa karkashin APC a zaben 2015.
El-Rufai ya ce kwata-kwata bai da sha'awar neman takarar amma tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tilasta masa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng

