Littafin IBB: Jigon APC Ya Fadi Dalilin Rashin Ganin Buhari wajen Taro
- An nemi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari an rasa a wajen ƙaddamar da littafin tarihin Ibrahim Badamasi Babangida
- Jigo a jam'iyyar APC a jihar Neja, Jonathan Vatsa, ya yi sharhi kan rashin ganin Buhari a wajen taron ƙaddamar da littafin
- Ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasan har yanzu yana jin zafin juyin mulkin da Janar IBB ya yi masa a shekarar 1985
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Wani jigo a jam'iyyar APC, Jonathan Vatsa, ya yi magana kan rashin halartar Muhammadu Buhari a taron ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Jonathan Vatsa ya danganta rashin halartar Buhari da jin zafin da yake yi kan juyin mulkin da Janar IBB ya yi masa a shekarar 1985.

Asali: Twitter
Jaridar Tribune ta rahoto cewa jigon na APC a jihar Neja ya bayyana hakan ne yayin da yake martani kan rashin ganin Buhari a wajen taron.

Kara karanta wannan
Ni ba Ba-Yarbe bane: IBB ya fadi gaskiyar karin sunan 'Babangida' a cikin sunansa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Buhari bai je wajen taron IBB ba?
A cewar Jonathan Vatsa, ƙin halartar Buhari ba abin mamaki ba ne, duba da irin raɗaɗin da juyin mulkin ya yi masa.
Jonathan Vatsa ya bayyana cewa juyin mulkin 1985 da Babangida ya jagoranta wani babban cin amana ce da ya yi matuƙar tasiri a rayuwar Buhari.
Haka kuma ya ƙara da cewa rashin halartar Buhari shaida ce ta yadda tsohon shugaban ƙasar yake ci gaba da jin haushin jihar Neja, inda Janar Babangida ya fito.
"Duk da irin goyon bayan da jihar ta ba Buhari a lokacin yaƙin neman zaɓensa, ya yi watsi da ita tare da ƙin aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa."
"Duniya gaba daya ta san cewa jihar Neja ta sha wuya a hannun Buhari saboda IBB. Tsawon shekaru takwas bai taɓa kai ziyarar aiki mai muhimmanci a jihar ba, kuma babu wani babban aikin gwamnatin tarayya da aka aiwatar."
“Aikin tashar jirgin ruwa ta Baro, wanda ya jawo cece-kuce a jihar kwanan nan, Buhari ya watsar da shi, tare da duk wasu manyan hanyoyin tarayya da ke jihar.”
“An tilastawa mutanen jihar su biya diyyar zunubin da ba su san komai game da shi ba. Ya ware jihar saboda laifin mutum guda."
- Jonathan Vatsa
Littafin IBB ya jawo muhawara
Taron ƙaddamar da littafin, wanda fitattun mutane suka halarta, ya jawo hankalin jama’a tare da jawo muhawara mai zafi.
Sai dai, Jonathan Vatsa ya ce ba zai yi tsokaci kan littafin ba har sai ya gama cikakken nazari a kansa.
IBB ya magantu kan kifar da Buhari
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi magana kan kifar da gwamnatin Muhammadu Buhari a shekarar 1985.
Janar IBB ya bayyana cewa matakin kifar da gwamnatin Muhammadu Buhari ya zama dole duba da yadda ƙasa ta taɓarɓare a lokacin.
Ya bayyana cewa Buhari da mataimakinsa a wancan lokacin, sun ware kansu daga sojoji da sauran al'umma.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng