Mutuwa Mai Yankar Ƙauna, Allah Ya Yi Wa Mahaifi da Kawun Ɗan Takarar Gwamna Rasuwa

Mutuwa Mai Yankar Ƙauna, Allah Ya Yi Wa Mahaifi da Kawun Ɗan Takarar Gwamna Rasuwa

  • Ɗan takarar gwamnan jihar Edo a inuwar LP a zaɓen 2024, Olumide Akpata ya tabbatar da rasuwar mahaifinsa da kawunsa
  • A wani sako da ya fitar ranar Litinin, 24 ga watan Fabrairu, 2025, tsohon shugaban NBA ya ce rashin waɗannan mutanen guda biyu ya girgiza shi
  • Akpata, wanda ya jima ba a ji ɗuriyarsa a soshiyal midiya ba, ya sha kaye hannun Monday Okpebholo na APC a zaben gwamnan Edo da aka yi a bara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Edo - Tsohon shugaban Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) kuma dan takarar gwamna a Edo a inuwar jam'iyyar LP a 2024, Olumide Akpata, ya yi rashin iyaye.

Akpata ya sanar da cewa Allah ya yi wa mahaifinsa Dr. Henry Akpata da kuma kawunsa Dr. Sunny Akpata rasuwa.

Olumide Akpata.
Mahaifi da kawun ɗan takarar gwamnan jihar Edo a zaɓen 2024, Olumide Akpafa sun kwanta dama Hoto: Olumide Akpata
Asali: Twitter

Ɗan takarar gwamnan ya daina magana

Kara karanta wannan

"Dole Tinubu ya samu nasara da ƙarfin ikon Allah," Minista ya hango abin da zai faru a 2027

Ɗan siyasar ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X karo na farko bayan tsawon lokaci ba a ji ɗuriyarsa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akpata, wanda ya nemi zama gwamna a zaben Edo na watan Satumba 2024, ya daina cewa komai kafafen sada zumunta tun bayan kammala zaben wanda APC ta yi nasara.

A watan Oktoba 2024, ya sanar da cewa ba zai kai ƙalubalanci nasarar Gwamna Monday Okpebholo a gaban kotun sauraron kararrakin zaben gwamna ba.

Akpata ya sanar da rasuwar mahaifi da kawunsa

A yau Litinin, 24 ga Fabrairu, 2025, Olumide Akpata ya bayyana dalilin da ya sa aka ji shi shiru na tsawon watanni huɗu.

"Lokacin yakin neman zabe, na rasa wani mutum mai matukar daraja a gare ni watau kawuna, Dr. Sunny Akpata, wanda ya kasance tamkar ubana na biyu a rayuwata.
"Saboda kacaniyar yakin neman zabe, ba mu samu damar yi masa girmamawar karshe ba sai a watan Nuwamba 2024."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta yi sabon gwamna a Najeriya, ya karbi rantsuwar kama aiki

Ya kara da cewa jim kadan bayan hakan, mahaifinsa Dr. Henry Akpata ya kamu da rashin lafiya mai tsanani, wanda ya tilasta masa mayar da hankali kan kula da shi.

Ya ce duk da kokarin likitoci, mahaifinsa ya rasu a ranar 10 ga Janairu, 2025, yana da shekaru 84 a duniya.

Olumide Akpata.
Tsohon ɗan takarar gwamnan Edo, Olumude Akpata ya yi rashin mahaifi Hoto: @OlumideAkpata
Asali: Twitter

Mutuwar mahaifi ta girgiza Akpata

Olumide Akpata ya bayyana mahaifinsa a matsayin ginshikin rayuwarsa da ya kula da shi da ‘yan uwansa cikin soyayya da kulawa tun bayan rasuwar mahaifiyarsu shekaru 33 da suka wuce.

"Mutuwarsa babban rashi ne a gare ni, amma na gode wa Allah da lokacin da muka yi tare da shi da irin tarbiyyar da ya bar mana.
"Wannan lokaci na juyayi ya kara fahimtar da ni cewa shugabanci ba shi da ma’ana idan ba tare da jin ƙan jama’a ba."

Ya ƙara da cewa yana nan tare da mutanen Edo da kuma al’ummar Najeriya, yana mai jaddada cewa zai dawo da karfi don ci gaba da fafutukar neman sauyin siyasa a jihar.

Kara karanta wannan

"Ba a shugaban APC zan dawwama ba," Abdullahi Abbas ya fadi kujerar da ya ke nema a kano

Tsagin LP ya ɗorawa Peter Obi laifi

A wani labarin, kun ji cewa tsagin jam'iyyar LP ya ɗora laifin rashin nasarar Olumide Akpata a zaɓen gwamnan jihar Edo kan Peter Obi.

Sakataren LP, Abayomi Arabambi ya ce tsohon gwamnan Anambra kuma ɗan takarar shugaɓan ƙasa a 2023 shi ne ya jawo jam'iyya ta sha kashi a hannun APC.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262