Shari'ar Yahaya Bello: Jami'an EFCC Dauke da Makamai Sun Mamaye Kotu a Abuja

Shari'ar Yahaya Bello: Jami'an EFCC Dauke da Makamai Sun Mamaye Kotu a Abuja

  • Jami’an EFCC sun mamaye babbar kotun tarayya, Abuja yayin da aka ci gaba da shari’ar tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello
  • A zaman kotu, shaidar farko ya tabbatar da cewa sunan Yahaya Bello bai bayyana a takardun kadarorin da ake bincike akai ba
  • Bayan gabatar da shaidu biyu, alkalin kotun, Mai shari’a Emeka Nwite ya dage sauraron karar zuwa ranar 6 da 7 ga watan Maris, 2025

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Jami’an EFCC sun mamaye babbar kotun tarayya da ke Abuja yayin da aka ci gaba da shari’ar tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello a ranar Litinin.

Jami’an hukumar sun rufe wata babbar hanya da motarsu, inda suke rike da bindigogi iri-iri, tare da takaita shigar mutane zuwa harabar kotun.

Kara karanta wannan

Sojoji, 'yan sanda da 'yan banga sun hadu sun gwabza artabu da 'yan bindiga

An ci gaba da shari'ar tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello da EFCC
Jami'an EFCC sun mamaye babbar kotun tarayya Abuja da aka ci gaba da shari'ar Yahaya Bello. Hoto: @OfficialGYBKogi, @officialEFCC
Asali: Twitter

Baya ga bindigogi, rahoton Punch ya nuna cewa jami'an sun jibge karnuka da wasu makamai a kofar kotun domin tsaurara tsaro a wurin shari’ar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ci gaba da shari'ar Yahaya Bello da EFCC

Lauyoyi da ke kotun sun nuna damuwa game da matakan tsaro na EFCC, suna tambayar dalilin mamaye kotun da jami’an suka yi.

A ranar 13 ga Disamba, 2024, kotun tarayya da ke Abuja ta ba da belin Yahaya Bello kan kudi Naira miliyan 500 tare da mutane biyu masu tsaya masa.

Ana zargin Yahaya Bello da almundahanar N80.2bn, amma tsohon gwamnan ya musanta dukkan tuhume-tuhumen da aka yi masa.

Lauyan da ke kare Bello shi ne Joseph Daudu, SAN, yayin da Kemi Pinheiro, SAN, ke jagorantar tawagar lauyoyin EFCC.

'Babu sunan Yahaya Bello' - Shaida a kotu

A zaman kotun na yau, shaidar farko, Segun Joseph Adeleke, ya ce sunan Bello bai bayyana a takardun kadarorin da ake bincike a kai ba, inji rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi ragargaza mai zafi, sun kashe 'yan ta'adda 82, sun kwato tarin makamai

Shaida ya shaidawa kotu cewa babu sunan Yahaya Bello a kadarorin da ake bincike a kansu
Wani shaida ya fadawa kotu cewa babu sunan Yahaya Bello a kadarorin da ake bincike kansu. Hoto: @OfficialGYBKogi
Asali: Facebook

Adeleke, wanda shi ne babban daraktan kamfanin Efab Properties, ya shaida wa kotu cewa bai taba ganin Yahaya Bello a lokacin cinikin kadarorin ba.

Da EFCC ta kira shaidar, lauyan Yahaya Bello, Joseph Daudu, ya nuna adawa, yana cewa sunan shaidar ba ya cikin jerin sunayen da aka bayar tun farko.

Duk da haka, shari’ar ta ci gaba, inda shaidar ya bayyana yadda aka sayi kadarori a No. 1, layin Ikogosi a Maitama da Gwarinpa.

Adeleke ya jaddada cewa sunan Yahaya Bello bai bayyana a kadarorin biyu ba, kuma bai taba ganin shi a lokacin cinikin ba.

Kotu ta dage shari'ar zuwa Maris

Shaida na biyu, Williams Abimbola, ya bayyana kansa a matsayin jami’in bin doka a bankin UBA.

Ya karanta takardun da aka bukata, ciki har da bayanan asusun gidan gwamnati na Kogi daga 2016 zuwa 2024 da wasu takardu.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ga ta kansa: An jero manyan ƴan siyasa 17 da suka fice daga jam'iyyar LP

Bayan shaidar ya kammala bayani, Mai shari’a Emeka Nwite ya dage shari’ar zuwa 6 da 7 ga watan Maris, 2025, don ci gaba da sauraron karar.

Yahaya Bello ya fito daga gidan kaso

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya samu ‘yanci bayan cika sharuddan belin da aka gindaya masa.

An sako shi daga gidan yarin Kuje bayan cika ka’idojin da kotun tarayya da ke Maitama, Abuja, ta gindaya, da suka hada da N500m da masu tsaya masa biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.