El Rufa'i zai Yi Zazzaga, zai Yi Hirar Farko bayan Sauka daga Gwamna
- Tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya sanar da cewa zai bayyana a wata hira kai tsaye a gidan talabijin
- Wannan shi ne karon farko da El-Rufa'i zai yi hira da kafar watsa labarai tun bayan barinsa mulki a Mayu 2023
- Jama’a sun tofa albarkacin bakinsu kan wannan sanarwa, inda wasu suka yaba, wasu kuma suka yi ta sukarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i, ya bayyana cewa ya amince da yin hira da gidan talabijin na ARISE.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa za a watsa hirar da zai yi ga 'yan Najeriya kai tsaye da misalin karfe 8 na dare.

Asali: Facebook
El-Rufa'i ya bayyana hakan ne a shafinsa na X, yana mai cewa wannan shi ne karon farko da zai yi hira da wata kafar yada labarai tun bayan barinsa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Kara karanta wannan
Mutuwa mai yankar ƙauna: Allah ya yi wa mahaifi da kawun ɗan takarar gwamna rasuwa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
El-Rufa'i: Hira ta farko tun bayan barin mulki
A cikin sanarwar da ya wallafa, El-Rufa’i ya ce tawagar sa ta yada labarai ta lura cewa bai taba yin wata hira ta musamman ba tun bayan barinsa mulki.
A cewarsa:
"Tawagar yada labarai na ta lura da cewa wannan shi ne karon farko da zan bayyana a wata hira tun bayan barin ofis.
Don haka, ina gayyatar kowa da kowa da ya saurari wannan hira."

Asali: Twitter
Ra’ayoyin jama’a kan sanarwar Nasir El-Rufa'i
Bayan da El-Rufa’i ya fitar da wannan sanarwa, mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu, wasu na yabawa yayin da wasu ke sukar matakin nasa.
Hon. Ezekiel Baba Kari ya bayyana jin dadinsa da wannan dama, yana mai cewa:
"Wannan abu ne mai kyau. Za mu saurari shirin. Wannan wata dama ce da za ka yi amfani da ita don wanke wasu kurakurai da jama’a ke yi a kanka. Allah ya kara maka albarka."

Kara karanta wannan
"Ba a shugaban APC zan dawwama ba," Abdullahi Abbas ya fadi kujerar da ya ke nema a kano
Idris Husseini ya bayyana yadda El-Rufa’i ya taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya, inda ya ce:
"Lokacin da na tuna yadda ka taimaka wajen kawo Buhari Villa a 2015, da yadda ka hana Atiku samun nasara a 2019,
"Sannan yadda Tinubu ya dogara da kai don samun goyon bayan Arewa, sai na yi mamakin ko Tinubu ya manta da haka.
"Mallam na jiya, shi ne mallam na yau da gobe. Allah ya kara maka karfi."
Sai dai wasu sun yi kakkausar suka, kamar yadda wani mai suna Alex Fabiyi ya yi wa El-Rufa’i ba'a, yana mai cewa:
"Yaushe za a gan ka a CNN, BBC ko Aljazeera? Idan har hakan ta faru, sai na saurara."
Haka kuma, wani Yusuf Abu Yazeed ya yi gargaɗi ga El-Rufa’i da cewa:
"Ka kula da duk abin da za ka fada. Ka sanya wa harshenka linzami."
El-Rufa'i ya yi magana kan cika shekaru 65
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya yi martani bayan an taya shi murnar cika shekaru 65 a makon da ya wuce.
El-Rufa'i ya yi godiya ga wadanda suka taya shi murna inda ya ce wasu sun ki taya shi murna har sai da Bola Tinubu ya bude musu kofa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng