'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari a Katsina, Sun Hallaka Bayin Allah
- Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun tafka ta'asa a jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
- Miyagun sun kai hare-haren ta'addanci a wasu ƙauyuka guda biyu na jihar Katsina a ranar Lahadi, 23 ga watan Fabrairun 2025
- Ƴan bindigan sun hallaka mutum uku waɗanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba bayan sun buɗe musu wuta ba ƙaƙƙautawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hare-hare kan ƙauyukan Gidan Sule da Kwana Doka a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina
Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindigan sun kashe mutane uku tare da raunata wasu mutum biyu, a hare-haren da suka kai a ranar Lahadi.

Asali: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan bindiga suka kai harin
Majiyoyi sun bayyana cewa hare-haren sun faru ne da misalin ƙarfe 10:00 na dare a ranar Lahadi, 23 ga watan Fabrairun 2025.
Ƴan bindigan waɗanda suke ɗauke da manyan makamai sun afkawa ƙauyukan, inda suka riƙa harbe-harbe ba kakkautawa.
"A Gidan Sule, an harbe mutane uku har lahira, sannan an kona gidaje da dama, yayin da a Kwana Doka, wasu mutane biyu sun samu munanan raunukan harbin bindiga kuma an garzaya da su babban asibitin Funtua domin duba lafiyarsu."
- Wata majiya
Bayan samun rahoton harin, tawagar sintiri ta ƴan sanda masu amfani da motar sulke (APC) sun hanzarta zuwa yankin Unguwar Ali/Kwankiro domin tare ƴan bindigan.
Jami'an tsaron sun yi artabu mai tsanani da ƴan bindigan, wanda ya tilasta musu tserewa zuwa cikin daji.
Waɗannan hare-hare sun ƙara dagula yanayin tsaro a yankin, inda al'ummar ke ci gaba da fuskantar barazanar ƴan bindiga.
Wannan yanayi na nuna yadda hare-haren ƴan bindiga ke ci gaba da yin illa ga rayuwar jama'a a yankin Arewa maso Yamma, tare da haifar da asarar rayuka, dukiyoyi, da kuma raba mutane da gidajensu.
Ƴan sanda sun jawo hankulan jama'a
Hukumar ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro na ci gaba da ƙoƙarin dakile waɗannan hare-hare, tare da yin kira ga jama'a da su ba da haɗin kai wajen samar da bayanai masu amfani domin taimakawa wajen kawo ƙarshen wannan matsalar.
Ana kuma jan hankalin jama'a da su kasance masu sanya idanu, tare da kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba ga hukumomin tsaro mafi kusa, domin ɗaukar matakan da suka dace.
Yana da muhimmanci a ci gaba da yin addu'a da kuma ɗaukar matakan tsaro na ƙashin kai, domin kare kai da iyalai daga hare-haren ƴan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuka.
Ƴan bindiga sun takurawa jama'a
Wani mazaunin ƙaramar hukumar Faskari, Hayatu Abdullahi, ya nuna damuwa kan yadda ƴan bindiga suke ta'addanci a yankunansu.
Ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro kan su kawo musu ɗauki domin shawo kan matsalar.
"Abin akwai ban takaici yadda ƴan bindiga suke ta'addancinsu. Ya kamata hukumomin tsaro su ƙara ƙaimi wajen kawo ƙarshen miyagun nan."
-Hayatu Abdullahi
Ƴan bindiga sun kai hari a Neja
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai harin ta'addanci a gidan wani sakataren ƙaramar hukuma a jihar Neja.
Ƴan bindigan a yayin harin da suka kai cikin tsakiyar dare, sun sace sakataren ƙaramar hukumar Munya tare da wasu mutum huɗu zuwa cikin daji.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng