'Ya Zama Dole': IBB Ya Fadi Musabbabin Kifar da Gwamnatin Buhari, Ya Jero Kura Kurai

'Ya Zama Dole': IBB Ya Fadi Musabbabin Kifar da Gwamnatin Buhari, Ya Jero Kura Kurai

  • Janar Ibrahim Babangida ya bayyana musabbabin kifar da tsohon shugaban kasa a Najeriya, Muhammadu Buhari
  • IBB ya ce sun kifar da gwamnatin Buhari a 1985 saboda ya mayar da mulki na kansa, tare da ware kansa daga sojoji da fararen hula
  • Janar Babangida ya bayyana cewa a 1985 sojoji sun fahimci cewa mulkin Buhari ya gaza, kuma rarrabuwar kawuna a rundunar soja na iya jefa kasa cikin hadari
  • Ya ce gwamnatin Buhari ta dauki matakai masu tsauri, tana keta hakkin jama’a, kuma hakan ya jefa al’umma cikin tsoro da kuncin rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida (mai ritaya), ya magantu kan kifar da mulkin Muhammadu Buhari.

Janar Babangida ya ce an kifar da gwamnatin Janar Muhammadu Buhari a 1985 saboda ya mayar da mulki na kansa.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya sake dagula siyasa, ya gana da shugabannin PDP, an yada hotunan ganawar

IBB ya fadi dalilin kifar da gwamnatin Buhari
Janar Ibrahim Babangida ya ce kifar da Buhari a mulki da ya yi ya zama dole. Hoto: Amintacciya, Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

'Musabbin kifar da gwamnatin Buhari' - IBB

IBB ya bayyana haka ne a cikin littafin tarihin rayuwarsa da aka kaddamar a Abuja a makon da ya gabata, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin littafin IBB ya yi tone-tone da dama musamman abubuwan da suka shafi mulkinsa da wayar da kan al'umma kan wasu zarge-zarge.

A cewarsa:

"Canjin shugabanci ya zama dole saboda yanayin ƙasar yana kara tabarbarewa, jama'a sun fara tsoron abin da ke tafe, kuma sojoji sun rabu."
"Janar Buhari da mataimakinsa, Janar Tunde Idiagbon, sun ware kansu daga sojoji da al’umma, sun kafa dokoki masu tsauri da keta hakkin jama’a."
"Jama’a sun fuskanci matsin tattalin arziki, kuma kayayyakin masarufi sun yi karanci, an kuma hana mutane ‘yancin su tare da tsauraran hukunci."

IBB ya kuma yi magana kan korar wasu sojoi da aka yi ba tare da bin ka'ida ba inda ya ce:

"An kori manyan hafsoshin soja ba tare da bin doka ba. Wannan ya haddasa rashin jituwa a tsakanin rundunar soja, wanda ke barazana ga kasa."

Kara karanta wannan

'Ya'yan Abacha sun yi martani bayan IBB ya yi maganganu kan mahaifinsu

"A karshe, sojoji sun yanke shawarar sauya shugabanci ba tare da zubar da jini ba, kuma a ranar 27 ga Agusta, 1985, na karbi mulki."
IBB ya fadi kura-kuran da Buhari ya yi a mulkinsa
Janar Ibrahim Babangida ya ce kifar da gwamnatin Buhari ya zama dole duba da kura-kuransa. Hoto: Muhammadu Buhari.
Asali: Twitter

IBB ya magantu kan kura-kuran Abacha

Tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana cewa daya daga cikin manyan kuskuren da ya yi a rayuwarsa shi ne barin Marigayi Janar Sani Abacha ya ci gaba da zama a cikin mulki bayan ya sauka a shekarar 1993.

Ya ce hakan ya hana dawowar mulkin farar hula, wanda ya jinkirta shirin mika mulki ga zababbun shugabanni.

Babangida ya bayyana wannan ne a wata hira, inda ya musanta zargin da ake yi cewa shi ne ya jinkirta zaben June 12 na 1993, wanda ya haifar da rikici a siyasar Najeriya.

Su wa suka fara jirkita zaben?

A cewarsa, wata kungiya da ba a san ta ba ce ta fara kokarin jinkirta zaben, ba wai umarninsa ba.

Kara karanta wannan

Yadda adawar manyan yan siyasar Najeriya za ta shafi tasirin gwamnatin Tinubu

A kalamansa kamar yadda TheCable ta ruwaito:

"Ba ni ne na jinkirta zaben ba. Wata kungiya ce da ba a san ta ba ta fara yin kira da a dage zaben, daga baya kuma hakan ya zama rikici a kasar."

Ya kuma bayyana cewa wasu gwamnoni da ‘yan siyasa ne suka bukaci a dage zaben shugaban kasa, amma daga baya suka zarge shi da shirin dadewa a mulki.

A cewarsa, wadannan ‘yan siyasa sun goyi bayan dage zaben ne a farko, amma daga baya suka juya masa baya tare da zarginsa da kokarin ci gaba da mulki.

Su wa suka bukaci a dage zaben?

Ya kara da cewa:

"Wasu daga cikin shugabannin siyasa da gwamnoni ne suka bukaci a dage zaben, amma daga baya su suka fara zargina da shirin ci gaba da mulki. Wannan abu ne da ya saba wa gaskiya."

A lokacin mulkinsa, Janar Babangida ya sha suka kan yadda aka soke zaben 1993, wanda masharhanta da dama ke ganin shine mafi inganci a tarihin Najeriya.

Kara karanta wannan

Obi ya fadi yadda salon mulkin IBB ya saɓa da sauran shugabannin Najeriya

Abiola ne ya lashe zaben

An bayyana zaben a matsayin wanda marigayi MKO Abiola ya lashe, amma daga bisani aka soke sakamakonsa, lamarin da ya haddasa tashin hankali a kasar.

Babangida ya ce yana da niyyar barin mulki, amma wasu manyan masu fada a ji a siyasance sun kawo matsin lamba wanda ya haddasa sauya akala.

Sai dai, ya ce barin Abacha a cikin mulki babban kuskure ne, domin hakan ya kara dagula komai tare da jinkirta komawar Najeriya zuwa mulkin farar hula.

IBB ya fadi makircin Abacha kan Abiola

Kun ji cewa tsohon Shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida, ya fallasa yadda marigayi Janar Sani Abacha ya shirya juyin mulki don hambarar da gwamnatinsa.

IBB ya bayyana cewa Abacha da mukarrabansa sun nuna ƙiyayya ga Abiola kuma sun shirya kashe shi idan ya zama shugaban ƙasa Read more:

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.