An yi arangama a Niger, Dan Sanda Ya Dirkawa Jami'ar Hukumar NIS Bindiga, an Tsare Wasu

An yi arangama a Niger, Dan Sanda Ya Dirkawa Jami'ar Hukumar NIS Bindiga, an Tsare Wasu

  • Wata jami’in shige da fice, Christian Oladimeji ta gamu da tsautsayi bayan yan sanda sun dirka mata harbi
  • An ce jami'ar ta jikkata sakamakon harbin da ‘yan sanda suka yi yayin da suka fuskanci farmaki daga wasu bata-gari a Minna
  • Yan sanda sun ce sun yi kokarin kwato kayan da ake zargi an sata, amma wasu ma’aikata da bata-gari suka kai musu hari suka lalata motarsu
  • Yayin da jami’an suka kokarin tserewa, wani dan sanda ya harba bindiga, harsashin ya samu Oladimeji a kafa, lamarin da ya sa ta fadi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Minna, Niger - Wata Mataimakiyar Sufritanda na Hukumar Shige da Fice, Christian Oladimeji, ya samu raunukan harbin bindiga a Minna, Jihar Neja.

Lamarin ya faru ne yayin wata hatsaniya wanda yan sanda suka harba bindiga bayan farmakin da wasu bata-gari.

Kara karanta wannan

Sojoji, 'yan sanda da 'yan banga sun hadu sun gwabza artabu da 'yan bindiga

Dan sanda ya harbi jami'ar shige da fice bisa kuskure a Niger
Wata jami'ar shige da fice ta samu raunuka bayan dan sanda ya harbe ya bisa kuskure. Hoto: Legit.
Asali: UGC

An yi kuskuren harbin jami'ar hukumar NIS

TheCable ta ce bata garin sun kai wa ‘yan sanda hari yayin da suke kokarin kwato kayayyakin da ake zargin an sata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani rahoto daga Sahara Reporters ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 12:30 na rana a ranar Juma’a 21 ga watan Fabrairun 2025.

Majiyoyi suka ce wata tawagar sintiri daga ofishin ‘yan sanda na ‘A’ division a Minna, karkashin jagorancin Ibrahim Paiko, na rangadin sintiri.

Jami'an na yawon ne lokacin da suka hango wasu ma’aikatan gine-gine dauke da sandunan karfe da ake zargin an sata.

Dan sanda ya yi kuskuren harbin jami'ar hukumar NIS
An tsare wasu bayan yan sanda sun harbi jami'ar hukumar NIS bisa kuskure. Hoto: Nigeria Immigration Service, Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

Yadda dan sanda ya kuskuri jami'ar hukumar NIS

"Da ma’aikatan suka hango ‘yan sanda, sai suka ajiye kayayyakin suka tsere, yayin da jami’an ke kokarin kwato kayan, wasu bata-gari sun afka musu da jifa."

- In ji rahoton.

Rahoton ya kara da cewa "harin ya lalata motar sintirin ‘yan sanda inda a yayin farmakin, ASP Ibrahim Audu ya harba bindiga, amma harsashin ya samu ASI Christian Oladimeji da ke wucewa akan babur.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta sanar da fara daukan 'yan sanda a karon farko a 2025

Harsashin ya samu Oladimeji a cinyarta, wanda ya sa ta fadi daga babur din tare da samun karin raunuka.

Nan take aka garzaya da ita Asibitin Kwararru na IBB a Minna, inda likitoci suka tabbatar cewa ba ta da ragowar harsashi a jikinta, amma ta samu karaya a kugunta.

An kama wasu mutane domin yi musu tambayoyi, yayin da aka fara bincike kan jami’an da abin da faru da su kan lamarin.

Hukuma ta bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu yayin da hukumomin tsaro ke ci gaba da kokarin tabbatar da doka da oda a jihar.

Zargin cin hanci: Hukumar NIS ya kori jami'anta

Kun ji cewa Hukumar shige da fice ta kasa ta dauki mataki mai tsauri kan jami'inta mai suna Okpravero Ufuoma kan bidiyonsa da ya yadu a kafafen sada zumunta.

Masu amfani da kafafen sada zumunta sun yada bidiyonsa yayin da aka nuna shi yana shirin karbar kudi a wajen matafiya a filin jirgin sama.

Rahotanni sun nuna cewa Shugaban hukumar shige da fice, Kemi Nandap ce ta bayyana dalilin daukan matakin a yau Alhamis, 8 ga watan Agustan 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.