Mutuwa Mai Yankan Kauna: Fitaccen Basarake Ya Rasu, Tinubu Ya Jajantawa Al'umma
- Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa mutanen Remo da Gwamnatin Ogun bisa rasuwar Oba Idowu Basibo, wanda ya shafe shekaru 22 yana mulkin Iperu
- Tinubu ya yaba wa Oba Basibo kan jagoranci na adalci da hakuri, yana mai cewa girmansa da hikimarsa za su kasance abin tunawa da ba za a manta da su ba
- Shugaban ya yi addu’a ga marigayin, yana fatan za a ci gaba da girmama bayansa, tare da dorawa kan kyawawan ayyukansa na al’umma
- Wannan na zuwa zuwa ne bayan tsohon sanata a jihar Ogun ya yi bankwana da duniya inda Gwamna Dapo Abiodun ya jajanta
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya miƙa ta’aziyyarsa ga al’ummar Remo da Gwamnatin Ogun bisa rasuwar fitaccen basarake a jihar.
Tinubu ya tura sakon ta'azziya bayan Oba Adeleke Adelekan Idowu Basibo, Sarkin Iperu da ya shekaru kan mulki ya riga mu gidan gaskiya.

Asali: Facebook
Tinubu ya jajanta bayan rasuwar basarake a Ogun
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan Bayani ya fitar da Tribune ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar, Tinubu ya ce:
"Oba Idowu Basibo ya shafe shekaru 22 yana zaman lafiya da kawo ci gaba a Akesan-Odoru."
Sanarwar ta ce Tinubu yana girmama Oba Basibo a matsayin uba na ƙwarai ga da dama, ciki har da Gwamna Dapo Abiodun, wanda ya fito daga yankin.
Tinubu ya yaba da marigayin a matsayin shugaba na gari da ya dage kan mulki, yana mai cewa al’ummarsa sun amfana da jagorancinsa.

Tinubu ya fadi alherin da marigayin ya yi
Shugaban ya tuna da martabar Oba Basibo da wayonsa, yana mai cewa shawarwarinsa za su ci gaba da zama abin tunawa a zukatan shugabanni.

Kara karanta wannan
Tazarce: Minista ya fadi jihar Arewa da Tinubu zai samu ruwan kuri'u a zaben 2027
Yayin da sarkin ke shirin gamuwa da Ubangijinsa,Tinubu ya nuna kwarin gwiwa cewa abin da ya bari zai ci gaba da ba da tasiri, cewar Leadership.
Tinubu ya kuma yi addu’a ga marigayin, yana fatan Allah ya jikansa da rahama, ya ba shi hutu har abada da kuma ba iyalansa hakurin jure wannan rashi.
'Ba za a manta da shawarwarin basaraken ba' - Tinubu
“Shawarar da ya ba shugabanni da ba su da iyaka cikin gaskiya da daraja za a tuna da su tare da girmamawa.”
- Cewar Bola Tinubu
Tsohon sanata ya yi bankwana da duniya
Mun ba ku labarin cewa mutane sun shiga alhini bayan tsohon sanatan Ogun ta Yamma, Ayodeji Otegbola ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 91 a duniya.
Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai, ƴan uwa da abokan arzikin mamacin tare da addu'ar Allah ya ba su haƙurin jure wannan rashi da suka yi.
Abiodun ya bayyana cewa mutuwar sanatan babban rashi ne ga jihar Ogun da ma Najeriya baki ɗaya, ya yi addu'ar Allah ya gafarta masa ya kuma yi masa rahama.
Asali: Legit.ng