'Sun So Kashe Shi': IBB Ya Fadi Makircin da Abacha Ya Shirya Masa da MKO Abiola

'Sun So Kashe Shi': IBB Ya Fadi Makircin da Abacha Ya Shirya Masa da MKO Abiola

  • Tsohon Shugaban kasa, Ibrahim Badamasi Babangida, ya fadi yadda marigayi Janar Sani Abacha ya shirya juyin mulki don hambarar da gwamnatinsa
  • Janar Babangida mai ritaya ya bayyana cewa Abacha da mukarrabansa sun nuna ƙiyayya ga Abiola kuma sun shirya kashe shi idan ya zama shugaban ƙasa
  • A cewarsa, soke zaɓen June 12 an kitsa shi ne ta "ƙungiyar" Abacha, kuma hakan ya hana yiwuwar shiga yaki bayan kashe Abiola

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon Shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya ya magantu kan yunkurin yi masa juyin mulki.

IBB ya bayyana cewa abokinsa na kusa, marigayi Janar Sani Abacha, ya shirya juyin mulki da karfi don hambarar da gwamnatinsa.

IBB ya yi tone-tone kan makircin da Abacha ya shirya masa
Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya fadi shirin marigayi Sani Abacha kan yi masa juyin mulki da kisa hallaka MKO Abiola. Hoto: John Harrington/Issouf Sanogo.
Asali: Getty Images

Yadda Abacha ya shirya makirci kan Abiola

Kara karanta wannan

"Najeriya ta yi rashi": Atiku da Malam El Rufai sun sake haɗuwa, bidiyo ya bayyana

Babangida ya bayyana hakan a littafinsa “A Journey in Service” da aka gabatar a birnin Abuja, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dattijon ya ce Abacha ya ƙi Chif M.K.O Abiola, wanda aka ce ya lashe zaɓen da aka soke na June 12.

A cewarsa, an kisa cewa idan Abiola ya zama shugaban ƙasa, Abacha da mutanensa sun shirya kashe shi.

Tsohon shugaban mulkin soja ya ce Abacha ya zama babban ciwon kai a lokacin da yake kokarin mika mulki ga farar hula.

Duk da cewa Abacha ya ceci rayuwarsa kuma ya taimaka masa wajen hawa mulki a 1985, Babangida ya ce janar ɗin mutum ne mai rikitarwa.

IBB ya yi tone-tone kan makircin da Abacha ya shirya masa

A cewarsa:

“Daya daga cikin manyan matsalolina a lokacin shine Sani Abacha, a ganina, zai goyi bayan shirin mika mulki, amma na yi kuskure.”
“Mun shaku da juna, har ya taɓa ceton rayuwata, amma mutum ne mai rikitarwa, wanda ba ka san me yake shiryawa ba.”

Kara karanta wannan

Obi ya fadi yadda salon mulkin IBB ya saɓa da sauran shugabannin Najeriya

Babangida ya ce Abacha da wasu sun fara yada magana a soja, suna nuna shi a matsayin matsala, domin su hambarar da gwamnatinsa ta hanyar juyin mulki.

Ya ce abin da ya fi ba shi mamaki shi ne irin ƙiyayyar da Abacha ke yi wa Abiola, wanda ya dauka suna da kyakkyawar alaka.

'Abacha ya shirya kisan Abiola' - IBB

A cewar Babangida, soke zaɓen June 12 an kitsa shi ne ta “ƙungiyar” Abacha, waɗanda da suka bari Abiola ya hau mulki, da sun kashe shi.

Ya ce:

“Sojojin da suka hada kai da shi suna da karfi. Idan Abiola ya zama shugaban ƙasa, da sun kashe shi. Kuma hakan zai iya jawo yakin basasa.”

Babangida ya ce yana da tsoron hakan, domin ya san irin wahalar da yaki ke haifarwa, a cewarsa, bai shirya ganin wani sabon yaki ba.

Peter Obi ya yabi salon mulkin IBB

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba da mamaki da ya tono wani sirri tsakaninsa da IBB a 1993

Kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ya ce Janar Ibrahim Babangida ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban tattalin arzikin Najeriya.

Obi ya yaba wa IBB bisa rubuta littafinsa, yana mai cewa jama'a za su koyi abubuwa da dama daga cikin littafin da aka wallafa.

Tsohon Gwamnan ya yaba wa Babangida bisa amincewa da nasarar MKO Abiola a zaben 1993, wanda zai hada kan jama'ar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

iiq_pixel