Gwamna a Arewa Ya Lashe Kyauta, Ya Zama Wanda Ya Fi 'Tsafta' a Najeriya
- Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya lashe lambar yabo a matsayin gwamnan da ya fi ƙoƙari a fannin tsaftar muhalli a Najeriya
- Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ne ya mikawa gwamnan lambar yabon a wani taro da aka shirya a fadar shugaban ƙasa
- Kwamishinan muhalli na Kaduna, Abubakar Buba, wanda ya wakilci Uba Sani ya yabawa al'ummar jihar bisa goyon bayan da suke ba gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna - Gwamnatin tarayya ta karrama gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, da lambar yabo ta gwamnan da ya fi kokari wajen tsaftar muhalli a Najeriya.
An ba shi lambar yabon ne sakamakon jajircewarsa wajen tsaftar muhalli, rage gurɓatar yanayi, da inganta rayuwar jama’a ta hanyar tsabtace garin Kaduna da kewaye.

Asali: Twitter
Kwamishinan muhalli da albarkatun ƙasa na jihar Kaduna, Abubakar Buba, ne ya karɓi lambar yabon a madadin gwamnan a ranar Talata, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan
El-Rufai ya sake dagula siyasa, ya gana da shugabannin PDP, an yada hotunan ganawar
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abubakar ya bayyana cewa wannan shi ne karo na biyu da jihar ke samun irin wannan girmamawa a 'yan kwanakin nan.
Yadda Gwamna Uba ke tsaftace Kaduna
Kwamishinan ya ƙara da cewa wannan kyauta ba wai kawai tana nuna nasarorin da aka samu ba, har ma tana ƙarfafa ci gaba da aiwatar da manufofi masu dorewa wajen kare muhalli.
Abubakar Buba ya jaddada cewa ƙungiyar "Clean Up Nigeria" ta ayyana Kaduna a matsayin mafi tsafta a yankin Arewa maso Yamma.
Haka nan kuma ya yaba da ƙoƙarin Gwamna Uba Sani wajen samar da hanyoyin magance matsalolin muhalli, ciki har da ɗaukar matakan rage gurɓatar iska da kuma share manyan titunan biranen Kaduna.
A cewarsa, gwamnatin Uba Sani ta ɗauki ma'aikatan share titi 2,400 domin tabbatar da tsaftar manyan birane a jihar.
Wannan shiri yana daga cikin dabarun da Gwamna Uba Sani ya bullo da su don tabbatar da cewa an inganta tsaftar muhalli da rage haɗarin kamuwa da cututtuka da ke da nasaba da datti.

Kara karanta wannan
"Yana raye ko ya mutu?": Watanni 3 ba a ga mataimakin gwamna ba, an fara tada jijiyoyin wuya
Gwamnatin Kaduna ta yabawa al'umma
Kwamishinan ya kuma yaba wa mazauna Kaduna bisa yadda suke zubar da shara ta hanyar da ta dace da ƙoƙarinsu na tsaftace muhallan da suke zaune.
Ya bayyana cewa muhalli mai tsafta yana taimakawa wajen rage yawaitar cututtuka kamar zazzabin cizon sauro, typhoid, da amai da gudawa.

Asali: Twitter
An ba Gwamna Uba Sani lambar yabon ne ta hannun Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), George Akume, a madadin Shugaba Bola Tinubu, a fadar shugaban ƙasa.
Wannan lambar yabo na nuna cewa jihar Kaduna ta zama ja gaba a fannin tsaftar muhalli, wanda hakan zai ƙarfafa sauran jihohi su bi sahun ta wajen inganta lafiyar muhalli.
Zaharadden Aliyu, wani mazaunin Kaduna ya shaidawa Legit Hausa cewa gwamna ya cancanci yabo kan yadda ake kwashe shara a bola a kai-akai.
Ya ce a yanzu gwamnati ba ta barin a tara shara da yawa har ta fara wari tana damun mutane.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30
Magidancin ya ce:
"Eh gaskiya Uba Sani yana ƙoƙarin wajen tsafta musamman batun shara, ya cancanci wannan karramawa.
"Za ka ga motocin kwashe shara sun zuwa a kan lokaci, da an tara shara a wurin da aka tanada, za ka ga an zo an kwashe, mutane kuma na ba da haɗin kai."
Gwamna Uba ya hango nasarar APC a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa Malam Uba Sani ya ce yana kwarin guiwar ƴan Najeriya za su sake dangwalawa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Gwamnan na Kaduna ya ce al’ummar Najeriya za su sake jefa kuri’a ga jam’iyyar APC saboda yadda take tafiyar da shugabanci cikin adalci wanda ke kawo ci gaba..
Asali: Legit.ng