EFCC: Kotu Ta Ƙara Takaita Tsohon Gwamnan CBN, An Kwae Miliyoyin Daloli da Kadarori
- Kotu ta karɓe Dala miliyan 4.7 da Naira miliyan 830 da ake tuhumar suna da alaƙa da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele
- Har ila yau kotun ta ƙwace wasu kadarori da suka hada da gidaje. filaye da sauransu a wurare daban,-daban. ta miƙa wa gwamnatin tarayya
- Mai shari'a Yellim Bogoro ne ya yanke hukuncin ranar Litinin, inda ya ce ya gamsu da bayanan EFCC cewa an mallaki kadarorin da kuɗin ta haramtacciyar hanya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Babbar kotun tarayya da ke Legas ta bayar da umarnin kwace Dala miliyan 4.7, Naira miliyan 830, da kuma kadarori da aka danganta da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
Mai shari’a Yellim Bogoro ne ya yanke wannan hukunci a ranar Juma’a, 21 ga watan Fabrairu, 2025 bayan ya amince da bukatar hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC).

Kara karanta wannan
Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30

Asali: Facebook
Hukumar EFCC dai ta buƙaci kwace waɗannan makudan kudi da kadarorin tare da mallaka su halak malak ga gwamnatin tarayya, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Emefiele: Kotu ta kwace makudan kudi
Wadannan kudade da aka kwace na cikin asusun bankuna daban-daban na wasu kamfanoni da ɗaiɗaikun mutane da suka hada da First Bank, Titan Bank, da Zenith Bank.
Kamfanonin sun haɗa da Omoile Anita Joy, Deep Blue Energy Service Limited, Exactquote Bureau De Change Ltd, Lipam Investment Services Limited, Tatler Services Limited, Rosajul Global Resources Ltd, da TIL Communication Nigeria Ltd.
Kadarorin Emefiele da aka ƙwace
Daga cikin kadarorin da kotu ta bayar da umarnin kwace su har da:
Gini mai hawa 11 da ke gaban Otunba Elegushi 2nd Avenue, Ikoyi, Legas, AM Plaza, filaye a yankin ƙaramar hukuma Amuwo Odofin a Legas da wani kamfanin haɗa kayan daƙi a Lekki.
Sauran sun haɗa gidaje biyu da aka sata daga kamfanin Chevron Nigeria da wasu gidaje da filaye da dama a Lekki da da Iƙoyi duk a jihar Legas.
Dalilin da ya sa aka miƙawa gwamnati
Mai shari’a Bogoro ya bayyana cewa duk wadannan kadarori da kudade an same su ne ta haramtattun ayyuka, don haka dole ne a maida su hannun gwamnatin tarayya.
A rahoton Channels tv, Alkalin ya ce:
"Ba kasuwancin halal ba ne. Anita Omoile kawar tsohon gwamnan babban bankin ƙasa, Godwin Emefiele ce wadda aka ba damar amfani da matsayinta wajen karkatar da dala daga CBN."

Asali: Facebook
Bisa haka, kotun ta yanke hukuncin cewa duk wadannan kadarori da kudade a mayar da su hannun gwamnatin tarayya.
Tsohon gwamnan CBN dai na ci gaba da fuskantar shari'a a gaban kotuna daban,-daban kan tuhume-tuhumen da suka shafi halatta kudin haram.
Kotu ta yi watsi da buƙatar Emefiele
A wani labarin, kun ji cewa kotun laifuka na musamman mai zama a Legas ta yi fatali da bukatar tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele.
Emefiele ta hannun lauyansa ya nemi dakatar da shari'ar da ke gaban kotun bisa dalilin cewa ba ta da hurumin sauraronta.
Asali: Legit.ng