Sojoji Sun Yi Ragargaza Mai Zafi, Sun Kashe 'Yan Ta'adda 82, Sun Kwato Tarin Makamai

Sojoji Sun Yi Ragargaza Mai Zafi, Sun Kashe 'Yan Ta'adda 82, Sun Kwato Tarin Makamai

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa dakarun sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta’adda 82, sun cafke masu laifi 198 a mako guda
  • Biyo bayan ragargazar 'yan ta'addan, sun ceto mutane 93 da aka yi garkuwa da su tare da kwace manyan makamai 86
  • Rundunar soji ta kuma kwato danyen mai da sauran kayayyaki da darajarsu ta kai sama da Naira miliyan 500 a yankin Niger Delta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rundunar sojojin Najeriya ta samu nasarar kashe 'yan ta’adda 82 tare da kama masu laifi 198 a cikin mako guda

Kazalika, dakarun tsaro sun ceto mutum 93 da aka yi garkuwa da su tare da kwace makamai 86 da harsasai sama da 2,000 daga hannun miyagu.

Kara karanta wannan

'Yan Shi'a fusata, sun ta aika kakkausan sako ga gwamnatin Tinubu

Janar Buba
Sojoji sun kashe 'yan ta'adda 82 a mako 1. Hoto: Defence Headquaters
Asali: Facebook

The Nation ta wallafa cewa Daraktan Hulda da Jama’a na Rundnar Tsaro, Manjo Janar Markus ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan ta'adda 41 sun mika wuya ga sojoji

Baya ga kisan 'yan ta’adda 82, Manjo Janar Kangye ya bayyana cewa mutane 41 daga cikin 'yan ta’adda sun mika wuya ga dakarun Operation Hadin Kai.

Ya ce wadanda suka mika wuya sun hada da maza 10, mata 12 da yara 19, inda sojoji suka karɓe su domin tantancewa.

Sojojin sun kuma samu nasarar cafke miyagu 198 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban, ciki har da satar mutane da fataucin makamai.

Manjo Janar Kangye ya ce ana ci gaba da bincike kan wadanda aka kama, kuma za a gurfanar da su a gaban kotu.

Sojoji sun kwato danyen mai a Niger Delta

Kara karanta wannan

Matashi ya gayyaci abokinsa gida ya masa kisan wulakanci da adda, ya sassara shi

A cewar Manjo Janar Kangye, sojojin da ke aiki a yankin Niger Delta sun samu nasarar kwato danyen mai da sauran kayayyakin mai da darajarsu ta kai sama da Naira miliyan 500.

Ya ce an samu wadannan kayayyaki ne daga hannun masu satar danyen mai da kuma wadanda ke tace shi ba bisa ka’ida ba.

Dangane da kwace kayayyakin mai, ya ce dakarun tsaro sun kwato:

  • Lita 366,530 na danyen mai da aka sace
  • Lita 117,320 na man dizil da aka tace ta haramun
  • Lita 600 na kalazir da aka sace

Bugu da kari, sojojin sun lalata wuraren tace mai 32 da suka hada da tankokin ajiya 60, rumbunan tace mai 38 da kuma motoci da jiragen ruwa da aka yi amfani da su wajen satar man.

Hafsun tsaro
Babban hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa. Hoto: Defence Headquaters
Asali: Facebook

Sojojin sun kwato makamai da harsasai

Manjo Janar Kangye ya kuma bayyana cewa sojojin sun kwace makamai iri-iri daga hannun miyagu a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Adamawa: 'Yan ta'adda sun kai hari babban asibiti, an yi awon gaba da bayin Allah

Ya ce makaman da aka samu sun hada da:

  • Bindiga kirar AK-47 guda 46
  • Bindigogi da aka sarrafa a gida guda 18
  • Bindigogi na gargajiya guda 19
  • Bindiga mai sarrafa kanta guda 3

Dangane da harsasai, ya ce sojojin sun kwato:

  • Harsasai 1,165 nau’in 7.62mm Special
  • Harsasai 128 nau’in 7.62mm NATO
  • Harsasai 600 nau’in 7.62 x 12.7mm

Dakarun Najeriya sun bayyana cewa za su ci gaba da kai farmaki kan 'yan ta’adda da sauran miyagu domin tabbatar da zaman lafiya a kasar nan.

Haka kuma, an bukaci al’umma da su rika ba da hadin kai ga jami’an tsaro domin tabbatar da nasarar yaki da ta’addanci da aikata laifuffuka.

Sojoji na farautar Bello Turji

A wani rahoton, kun ji cewa dakarun sojin Najeriya na bin diddigin dan ta'adda, Bello Turji da ya fitini al'umma a Arewa ta Yamma.

Shugaban sojin kasan Najeriya ne ya bayyana haka yayin da ya kai ziyara da ta farko jihar Zamfara domin karfafa dakarun soji kan yaki da ta'addanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng