Wasu Matsafa Sun Tona Kabari Sun Sace Gawa a Makabartar jihar Borno

Wasu Matsafa Sun Tona Kabari Sun Sace Gawa a Makabartar jihar Borno

  • An ruwaito cewa wasu da ake zargi da masu amfani da sassan jikin mutane sun shiga makabarta a Maiduguri, sun bude kabari
  • Al’ummar yankin makabartar Ramon Yashi sun gano kabari da aka bude ba tare da gawar cikinsa ba da suka ziyarci makabartar
  • A karkashin haka, mutanen yankin makabartar sun bukaci hukumomin tsaro da gwamnatin Borno su dauki mataki kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Al’ummar Maiduguri sun nuna damuwa kan yadda wasu da ake zargi da masu amfani da sassan jikin mutane ke tono gawarwaki a makabartu.

Rahotanni sun nuna cewa an samu kabari da aka tona a makabartar Ramon Yashi, inda aka gano cewa gawar da ke ciki ta yi batan dabo.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda na kara karfi, sun kai hari kan jami'an tsaro inda ake zargin Turji ya boye

Makabarta
An koka kan sace gawa a makabartar Borno. Hoto: Hugh Kinsella Cunningham
Asali: Getty Images

Zagazola Makama ne ya wallafa bayanan a shafinsa na X inda ya bayyana cewa al’ummar yankin sun bukaci hukumomin tsaro su dauki matakin gaggawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano kabari da aka bude babu gawa

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa sun gano kabari da aka bude amma babu gawa a cikinsa.

Mutumin ya ce:

“Mun ga gawar wani a cikin ruwa, amma da muka koma makabarta sai muka gano wani kabari da aka tono, amma babu gawar cikinsa,”

Hakan ya jefa al’ummar yankin cikin tsoro da fargaba, inda ake zargin cewa wasu da ke yin tsafi da sassan jikin mutane ne suka aikata wannan danyen aiki.

A cewar mazauna yankin, wannan ba shi ne karo na farko da irin wannan abu ya faru ba, sai dai wannan karon al’amarin ya fi tayar da hankali.

Kara karanta wannan

DSS ta gano makamai a ofishin hadimin tsohon shugaban majalisar Legas

Al’ummar yankin sun bukaci daukar mataki

Bayan wannan mummunan lamari, mutane da dama sun bukaci hukumomin tsaro su dauki mataki domin hana ci gaba da wannan ta’asa.

Wasu sun bukaci gwamnatin jihar Borno ta sanya idanu sosai kan makabartu domin hana masu aikata irin wannan mummunan aiki.

Haka zalika, wasu malaman addini sun bukaci a kara tsaurara tsaro a yankunan da ake samun irin wadannan abubuwa domin hana cin zarafin gawarwaki.

Wani malami a yankin ya bayyana cewa irin wannan aika-aika na iya kawo bala’i, yana mai kira ga jama’a su yi addu’a tare da daukar matakan kariya.

Zulum
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum. Hoto: Ahmad Hassan
Asali: Original

Fatan al'umma kan hukumomin Borno

Biyo bayan koke-koken al’ummar yankin, ana sa ran hukumomin tsaro za su gudanar da bincike domin gano wadanda ke da hannu a wannan aika-aika. .

Al’ummar yankin na fatan hukumomi za su kama wadanda suka aikata wannan danyen aiki tare da tabbatar da cewa ba a sake samun irin hakan a gaba ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun ƙaro rashin imani, sun kashe mutane kusan 20 a garuruwa 2

Har yanzu ana jiran karin bayani daga mahukunta kan matakin da za a dauka domin magance wannanar matsalar.

AfDB ya mika tallafi a jihar Borno

A wani rahoton, kun ji cewa bankin raya Afrika na AfDB ya raba tallafin Dala miliyan 1 domin sayen kayan abinci a jihar Borno.

An raba tallafin ne a wata hadin gwiwa da aka yi tsakanin AfBD da majalisar dinkin duniya domin tallafawa mutane a Arewa maso Gabas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng