Bayan Karyewar Farashin Abinci, Naira Ta Tumurmusa Dala a Kasuwar Canji a Najeriya

Bayan Karyewar Farashin Abinci, Naira Ta Tumurmusa Dala a Kasuwar Canji a Najeriya

  • Darajar Naira ta karu zuwa 1,494.03/$1 a kasuwar hukuma da 1,510.00/$1 a kasuwar bayan fage, sakamakon matakan da CBN ya dauka
  • CBN ya tsawaita siyar da dala ga ‘yan canji har zuwa Mayun 2025, wanda zai jawo wadatar dala tare da cire tsoron hauhawar farashi
  • Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya ce ana bin ingantattun manufofin kudi don rage daidaita kasuwar musayar kudade a Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Naira ta ƙara daraja a kasuwar canji ta hukuma, inda ta kai 1,494.03/$1 a ranar Alhamis, kamar yadda kasuwar hada-hada ta FMDQ ta bayyana.

Haka nan, a kasuwar bayan fage, Naira ta tashi zuwa 1,510.00/$, wanda ya rage bambanci tsakanin farashin hukuma da na kasuwa zuwa 15.5/$.

Darajar Naira ta karu a kasuwar hada hadar kudi ta gwamnati da ta bayan fage
An samu faduwar darajar Dala, inda Naira ta lula sama zuwa N1,494/$1. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Darajar Naira ta karu a kan Dala

Kara karanta wannan

Zamfara: Sojoji sun lalata sansanin rikakken dan ta'adda, sun kwashe buhunan abinci

Ana samun raguwar bambanci tsakanin kasuwannin musayar kudi sakamakon tsare-tsaren bankin CBN na inganta kasuwar musayar kudin, inji rahoton Daily Trust.

Rahoton kungiyar bincike ta CardinalStone ya nuna cewa Naira ta ƙara daraja da kashi 1.04% a kasuwar hukuma, yayin da ta ƙaru da 1.66% a kasuwar bayan fage.

A ranar da ta gabata, Naira ta samu ƙarfi, inda ta karu da 0.05% a kasuwar hukuma zuwa 1,509.53/$, sannan a kasuwar bayan fage ta tashi da 0.65% zuwa 1,535.00/$.

'Yan canji sun jinjinawa manufofin CBN

Matakin CBN na ci gaba da sayar da dala ga masu canji har zuwa 30 ga Mayun 2025, na ɗaya daga cikin dalilan da ke ƙarfafa Naira.

Gwamnan CBN, Cardoso ya magantu kan karfafa darajar Naira a kasuwar canji
Gwamnan CBN, Cardoso ya jaddada aniyarsa ta karfafa darajar Naira a kasuar canji. Hoto: @cenbank
Source: Twitter

Shugaban kungiyar 'yan canjin kuɗi, Aminu Gwadebe, ya ce matakin na CBN yana sanya dalar ta wadata a kasuwa tare da rage tsoron hauhawar farashin kudin.

Aminu Gwadebe ya ce:

"Sayar da kudin musaya daga bankuna zuwa masu canji na taimakawa wajen samar da isassun dala da hana tashin farashi."

CBN ya fadi tsare-tsaren daga darajar Naira

Kara karanta wannan

EFCC: Kotu ta ƙara takaita tsohon gwamnan CBN, an kwace miliyoyin daloli da kadarori

A gefe guda, tashin Naira ya zo ne a daidai lokacin da kwamitin tsare-tsaren kuɗi na CBN ya yanke shawarar barin matsakaicin kaso a 27.50%

Kwamitin ya kuma bar iyakar sauyin farashin kudade a kan +500 da -100, yayin da adadin ajiyar bankuna ya kasance 50%, da 16% ga bankunan 'yan kasuwa, da kuma ƙimar ruwa a 30%.

Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya ce kasuwar musayar kuɗi tana daidaituwa kuma za su ci gaba da bin hanyoyin da aka saba wajen tafiyar da manufofin kuɗi.

Jaridar Punch ta rahoto Cardoso yana cewa:

"Mun ga tasirin waɗannan matakan, kuma sakamakon yana tafiya cikin alkibla mai kyau. Za mu ci gaba da sa ido tare da tabbatar da cewa ba za mu ɗauki wani abu da wasa ba."

Cardoso ya ƙara da cewa babbar manufar CBN ita ce rage hauhawar farashin kaya daga adadi mai yawa zuwa ƙasa don inganta tattalin arzikin ƙasa.

N1510/$: Abin da ƴan canji ke cewa

Wani ɗan canji a Legas, Musa Lawal Bakori, wanda ya zanta da Legit Hausa, ya ce farashin $1 a kasuwar ƴan canji ya sauka zuwa kasa da N1,505, N1510, N151, gwargwadon yawan kudin.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ga ta kansa: An jero manyan ƴan siyasa 17 da suka fice daga jam'iyyar LP

Ya ce a yanzu suna sayen dalar Amurka a kan N1,490 zuwa N1,500 sannan suna sayar wa N1510, wasu lokutan sama da hakan idan kayan na da yawa.

Ko da aka tambaye sa abin da ya ke gani kan matakan gwamnati da CBN na karya farashin dala, Bakori ya ce:

"Matakan da CBN ke dauka, musamman na sayarwa 'yan canji dala kai tsaye yana taimaka mana wajen samuwar dalar cikin sauki, domin har yanzu tana wahala a kasuwar.
"Ka san, da zarar dala ta wadata, to farashinta na karyewa. Sannan akwai wadanda ke shigo da ita daga waje, idan za su dawo gida daga kasuwanci ko karatu.
"Farashin dalar zai iya ci gaba da faduwa kasa nan gaba, ma damar CBN ya ci gaba da daukar matakan, sannan ana samun kayan a kasuwa."

Abin da ke jawo karuwar darajar Naira

A wani labarin, mun ruwaito cewa, babban bankin Najeriya ya dauki wasu kwararan matakai da suka jawo darajar Naira take ci gaba da lulawa sama.

Wasu daga cikin matakan CBN sun hada da bullo da tsarin EFEMS da ya haɗa duk tsofaffin hanyoyin musayar kuɗi na hukuma zuwa tsari guda ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com