Atiku, Obasanjo da Kusoshin Najeriya Sun Dura Abuja, IBB Zai Fitar da Babban Sirri

Atiku, Obasanjo da Kusoshin Najeriya Sun Dura Abuja, IBB Zai Fitar da Babban Sirri

  • Manyan shugabannin Najeriya, ciki har da Atiku Abubakar da Olusegun Obasanjo, sun hallarci kaddamar da littafin rayuwar IBB
  • An shirya kaddamar da littafin mai suna 'A Journey in Service' a yau Alhamis, inda Ibrahim Babangida zai tona badakalar 12 ga watan Yuni
  • Olusegun Obasanjo zai jagoranci taron, yayin da Shugaba Bola Tinubu zai kasance babban bako na musamman, tare da fitattun shugabanni
  • Fitattun 'yan kasuwa da aka ce sun samu halartar taron sun hada da Alhaji Aliko Dangote, Abdulsamad Rabiu BUA da dai sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Manyan shugabannin Najeriya, ciki har da Atiku Abubakar da Olusegun Obasanjo, sun taru a Abuja don girmama tsohon shugaban mulkin soja, Ibrahim Babangida.

Idan ba a manta ba, Legit Hausa ta rahoto cewa IBB ya shirya kaddamar da littafin rayuwarsa wanda zai warware wasu batutuwa da suka shigewa mutane duhu.

Obasanjo, Atiku sun dura Abuja wajen kaddamar da littafin IBB
IBB zai kaddamar da littafin rayuwarsa yayin da Obasanjo, Atiku suka dura Abuja. Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Atiku ya dura birnin tarayya Abuja

Kara karanta wannan

IBB ya yi fallasa kan zaben 1993 da aka rusa, ya fadi rawar da Buhari ya taka a baya

Atiku ya kai ziyarar girmamawa ga Babangida a ranar Laraba, kafin kaddamar da littafin, inda ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Baya ga Atiku, ana sa ran wasu fitattun ‘yan siyasa da shugabanni za su halarta domin nuna girmamawa ga tsohon shugaban kasar.

An shirya kaddamar da littafin mai suna A Journey in Service a ranar 20 ga Fabrairun 2025 a dakin taro na otel din Transcorp Hilton, Abuja.

Babangida ya rubuta littafin don tunawa da shekaru 32 da barinsa mulki, tare da gudanar da taron tallafa wa gidauniyar dakin karatu na shugaban kasa.

Wasu shugabanni da za su halarci taron

Olusegun Obasanjo zai jagoranci taron yayin da Shugaba Bola Tinubu zai kasance babban bako na musamman, inji rahoton PM News.

Baya ga shugabannin Najeriya, ana sa ran mahalarta daga kasashen ketare, ciki har da manyan jami’ai daga Afirka da Turai.

Tsohon shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo, zai gabatar da jawabi, yayin da Yemi Osinbajo zai nazarci littafin, wanda zai tabo zaben 12 ga Yunin, 1993.

Kara karanta wannan

Matashi ya gayyaci abokinsa gida ya masa kisan wulakanci da adda, ya sassara shi

BUA, Dangote za su ba ta tallafin kudi

Ana sa ran tsoffin shugabannin kasa Muhammadu Buhari, Yakubu Gowon, Abdulsalami Abubakar, da Goodluck Jonathan za su halarta.

Tsohon ministan tsaro, Theophilus Danjuma, da shugaban kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, sun kasance a cikin manyan masu tallafawa taron.

Hakazalika, an rahoto cewa shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya yi alkawarin bayar da tallafin N2bn duk shekara na tsawon shekaru hudu don gina dakin kararatun.

Baya ga kaddamar da littafin, za a gudanar da tattaunawa kan tarihi da tasirin mulkin Babangida a kan siyasar Najeriya.

Atiku ya wallafa bidiyon isarsa dakin taron. Duba bidiyon a kasa:

IBB ya fallasa abin da ya faru a 12 ga Yuni

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya tabbatar da cewa marigayi MKO Abiola ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga Yuni, 1993.

IBB ya bayyana wannan a cikin littafinsa mai suna 'A Journey in Service', wanda aka ƙaddamar da shi a Abuja, birnin tarayya.

Tsohon Shugaban Ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya yi kira da a ci gaba da rubuta tarihin rayuwa duk da kalubalen da za a iya fuskanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.