Yadda Sojoji ke Bin Diddigin Bello Turji domin Kawar da Shi a Doron Kasa
- Shugaban rundunar sojojin kasa, Laftanal Janar Olufemi Oluyede, ya ce sojoji na bin Bello Turji kuma zai mutu ba da jimawa ba
- Laftanal Janar Olufemi Oluyede ya ce rundunar soji ta kashe shugabannin ‘yan bindiga da dama a Arewa maso Yamma a halin yanzu
- Haka zalika ya bukaci ‘yan Najeriya su hada kai da jami’an tsaro ta hanyar bayar da bayanai kan ayyukan ‘yan ta’adda a lungu da sako
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da yaki da ‘yan bindiga a jihar Zamfara da kewaye.
Shugaban sojojin kasa, Laftanal Janar Olufemi Oluyede, ya ce da izinin Allah za a kawar da fitaccen jagoran ‘yan bindiga, Bello Turji.

Kara karanta wannan
"Tinubu mutumin kirki ne, yana da niyya mai kyau," Babban malami ya yi wa mutane Nasiha

Asali: Twitter
Rahoton gidan talabijin din Channels ya nuna cewa Laftanal Janar Oluyede ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da manema labarai a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji na bibiyar dan ta'adda Bello Turji
Laftanal Janar Olufemi Oluyede ya bayyana cewa sojojin Najeriya na bibiyar kasurgumin dan ta'adda Bello Turji a ko’ina yake boye.
Punch ta wallafa cewa shugaban sojojin ya ce:
“Turji ya gudu, amma duk inda ya tafi, sai mun bishi. Kawai lokaci ne ya rage, za a kawar da shi daga doron kasa.”
Laftanal Janar Olufemi Oluyede ya kara da cewa an samu nasarar kashe wasu shugabannin ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma a ‘yan watannin nan.
Daga cikin wadanda aka kashe akwai Samaila, Boga da Boderi, wadanda dukkansu sun rasa ransu a hannun sojojin Najeriya.
Kokarin sojoji na samar da zaman lafiya
Shugaban sojojin ya ce rundunar na aiki tukuru domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a yankin.
“Za mu ci gaba da bin ‘yan ta’adda domin tabbatar da cewa Arewa maso Yamma ta zama yankin da ke da kwanciyar hankali.”
- Laftanal Janar Olufemi Oluyede
Sai dai duk da haka, Laftanal Janar Oluyede ya amince da cewa akwai wasu matsaloli da ke fuskantar sojojin a filin daga.
Amma kuma ya tabbatar da cewa sojojin za su shawo kan wadannan kalubale tare da ci gaba da yaki da ‘yan ta’adda.

Asali: Facebook
Sojoji sun bukaci hadin kan jama’a
Laftanal Janar Oluyede ya bukaci ‘yan Najeriya su ba da hadin kai ga jami’an tsaro domin samun bayanai kan ayyukan ‘yan bindiga.
A cewar shugaban sojojin:
“Idan jama’a suka rika taimakawa da sahihan bayanai, hakan zai taimaka wajen magance matsalar tsaro.”
A yayin ziyarar tasa, shugaban sojojin ya duba ofisoshin sojoji sannan ya karbi bayani daga kwamandan rundunar, Manjo Janar Oluyinka Soyele.
An ruwaito cewa wannan ziyara ita ce ta farko da Oluyede ya kai tun bayan nadinsa a matsayin shugaban sojoji a ranar 30 ga watan Oktoba, 2024.
Amurka za ta tallafawa Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Amurka za su cigaba da taimakwa Najeriya wajen yaki da 'yan ta'adda a fadin kasar nan.
Hakan na zuwa ne yayin da wani dan majalisar Amurka ya ce an yi amfani da kudin tallafin USAID wajen daukar nauyin 'yan ta'addan Boko Haram.
Asali: Legit.ng