Gwamnatin Tinubu Ta Kaddamar da Kwamishinonin Haraji Guda 50

Gwamnatin Tinubu Ta Kaddamar da Kwamishinonin Haraji Guda 50

  • Rahotanni na nuna cewa wamnatin Tarayya na kokarin fadada tsarin biyan haraji tare da dakile masu gujewa biyan haraji a fadn kasar nan
  • Ministan Kudi, Wale Edun, ya kaddamar da kwamitin sauraron karar haraji mai mutum 50 domin magance sabani da karfafa tattalin arziki
  • Hakan na zuwa ne yayin da ake sa ran majalisar dokoki za ta amince da kudirin gyaran haraji kafin karshen wannan watan da muke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rahotanni sun tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta dauki matakin dakile masu gujewa biyan haraji a Najeriya.

Ministan Kudi, Mista Wale Edun, ne ya bayyana hakan yayin kaddamar da sabon kwamitin sauraron karar haraji (TAT) a Abuja.

Bola Tinubu
Gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin haraji mai mutum 50. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Ma'ikatar yada labaran Najeriya ta wallafa a shafinta cewa an gudanar da taron ne a ranar Laraba da ta gabata.

Kara karanta wannan

Adamawa: An shiga fargaba da bindiga ta tashi a wurin ibada, mutane sun jikkata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kaddamar da kwamishinonin na cikin shirin gwamnati na kara habaka kudin shiga don bunkasa manyan sassan tattalin arziki kamar kiwon lafiya da ilimi.

Aikin kwamishinonin harajin Najeriya

Ministan Kudi, Wale Edun, ya ce kafa wannan kwamitin na da nufin tabbatar da adalci a tsarin haraji tare da magance duk wata takaddama da ke tsakanin gwamnati da ‘yan kasuwa.

Wale Edun ya ce:

“Dakile masu gujewa biyan haraji yana da matukar muhimmanci don kara karfafa tsarin haraji da kuma taimakawa ci gaban kasa.”

Kwamitin na da mutum 50 kuma zai raba aiki a shiyyoyi guda shida na kasar nan, ciki har da ofisoshi a Legas da Abuja, domin tabbatar da aiwatar da shirin cikin sauki.

Gwamnati na kokarin fadada tsarin haraji

Edun ya ce gwamnati na aiki tukuru don ganin an kara yawan masu biyan haraji a Najeriya, tare da kawar da duk wata dabara da za ta ba wasu damar gujewa biyan kudin da ya kamata su biya.

Kara karanta wannan

Yadda Sanatoci suka jawo hankalin Tinubu ya waiwayi gyaran titunan Arewa

Ministan ya ce:

“Guje wa biyan haraji na rage amana ga tsarin haraji kuma yana haifar da cikas ga ci gaban kasa. Za mu dauki matakan hana hakan.”

Majalisa na daf da yarda da kudirin haraji

Ana sa ran majalisar dokoki za ta kammala duba kudirin gyaran haraji a mako mai zuwa, bayan da kudirin ya riga ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa da majalisar wakilai.

Za a gudanar da zaman jin ra’ayin jama’a a ranar Litinin da Talata a majalisar dattawa, yayin da majalisar wakilai za ta yi nata zaman a ranar Laraba.

Majalisar ta tabbatar da cewa kafin karshen wannan wata za a amince da kudirin domin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu.

Wale Edun
Ministan kudin Najeriya, Wale Edun. Hoto: Aso Villa
Asali: Getty Images

Ministan Kudi ya kuma bayyana cewa tattalin arzikin kasar na samun sauyi, inda ya ce hauhawar farashin kayayyaki na raguwa, farashin abinci na saukowa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta fara kokarin kawar da kungiyoyi masu alaka da ta'addanci a jihar

Wale Edun ya ce hakan na nuna nasarorin da gwamnatin Tinubu ke samu a kokarinta na farfado da tattalin arziki, samar da ayyukan yi, da rage fatara a kasar nan.

Gwamnati za ta inganta rayuwar ma'aikata

A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya ce gwamnatin tarayya na shirin inganta rayuwar 'yan Najeriya.

Sanata Kashim Shettima ya bayyana shirye shiryen da gwamnatin ke yi domin inganta rayuwar ma'aikata da matasan kasar nan a nan gaba kadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

iiq_pixel