Kotu Ta Dakile Shirin Trump kan Yan Gudun Hijira game da Yancin Zama Ɗan Kasa

Kotu Ta Dakile Shirin Trump kan Yan Gudun Hijira game da Yancin Zama Ɗan Kasa

  • Kotun daukaka kara ta ki dage dakatarwar da aka sanya kan umarnin Donald Trump na hana 'yancin zama ɗan ƙasa ga wasu 'ya'yan 'yan gudun hijira
  • Kotun ta ce za a ci gaba da nazarin karar, inda ake sa ran za a yi muhawara a watan Yuni, lamarin da ka iya kaiwa Kotun Koli
  • Gwamnatin Trump na so ta hana haihuwa a Amurka zama tushen ɗan ƙasa ga yaran da iyayensu ba su da takardun izinin zama a ƙasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, Amurka - Kotun daukaka kara ba ta amince da yunƙurin gwamnatin Donald Trump na kawo ƙarshen 'yancin zama ɗan ƙasa ga wasu yaran 'yan gudun hijira ba.

Rahotanni sun ce wannan matakin kotu na iya kaiwa shari'ar Kotun Koli domin karkare shari'ar a can.

Kara karanta wannan

Kisan Hafsah: 'Malamin addinin musulunci' ya shiga matsala, an tasa ƙeyarsa zuwa gidan yari

Kotu ta ki amincewa da umarnin Trump kan Yan gudun hijira
Kotun Daukaka Kara ta ki dage hukunci kan umarnin Trump na dokar zama ɗan kasa ga yan gudun hijira. Hoto: @POTUS.
Asali: Getty Images

Kotu ta kawo cikas ga Trump kan umarninsa

Kotun ta ƙi bukatar Ma'aikatar Shari'a ta Amurka da ke neman a dage dakatarwar, cewar jaridar CNN.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan da wani alƙali a Seattle ya sanya hannu kan umarnin Trump, bayan da ya ce ya sabawa kundin tsarin mulki.

Kwamitin alƙalan kotun wanda ya ƙunshi wanda Trump ya naɗa da wanda Carter ya naɗa da kuma wanda Bush ya naɗa ya ce nazarin shari’ar zai ci gaba da gudana.

Ana sa ran shari’ar za ta shiga matakin hujjoji a watan Yunin wannan shekara da muke ciki.

Shari’ar da ke gaban kotun daukaka kara da ke San Francisco na daga cikin manyan shari’o’in da ke kalubalantar manufofin Donald Trump kan 'yancin zama ɗan ƙasa.

Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta ce umarnin Trump na game da 'yancin zama ɗan ƙasa yana da muhimmanci wajen gyara tsarin shige da fice da kuma magance rikicin kan iyaka.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi kaca kaca da gwamnatin Tinubu, ya tona makircin da APC ke kullawa a Osun

Yadda tsarin mulki yake kan dokar zama ɗan kasa

Tun shekarar 1868, kundin tsarin mulki da wata doka sun bai wa kowane mutum da aka haifa a Amurka 'yancin zama ɗan ƙasa, ba tare da la’akari da matsayin iyayensa ba.

Trump na so ya hana hakan ga yaran da iyayensu ba su da izinin zama ko kuma masu biza ta wucin gadi, AP News ta ruwaito.

Shari’ar ta samo asali ne daga ƙarar da attajiran lauyoyi na jihohi huɗu da jam’iyyar Democrat ke jagoranta suka shigar, inda suka kalubalanci yunƙurin gwamnatin Trump kan batun.

A cikin hujjojinsu, lauyoyin sun ce wannan ba batun shige da fice ba ne, sai dai batun 'yancin zama ɗan ƙasa da kundin tsarin mulki ya bayar, ba tare da ikon shugaban ƙasa ya canza ba.

Amurka za ta binciki daukar nauyin ta'addanci

Kun ji cewa Gwamnatin Amurka za ta binciki tallafin da ta bai wa Najeriya da wasu kasashe domin gano yadda aka yi amfani da su.

Wannan ya biyo bayan Sanata Scott Perry ya yi zargin cewa tallafin USAID na taimakawa kungiyoyin ta’addanci kamar Boko Haram da ISIS.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.