Katsina: Bayan Hana Caca, Karuwanci, Hisbah Ta Juyo kan Gidajen Casu, Ta ba da Umarni
- Hukumar Hisbah a jihar Katsina ta haramta duk wani ayyukan gidajen hala da dare a fadin jihar.
- Wannan mataki ya biyo bayan kokarin kare dabi'u da kiyaye tsaron al'umma musamman da dare a fadin jihar
- Kwamandan Hisbah, Aminu Usman, ya bukaci masu gidajen badala su rufe wuraren su, y ce duk wanda ya saba doka zai fuskanci hukunci
- Hisbah ta bukaci hukumomin tsaro su tabbatar da bin wannan umarni kamar yadda ta haramta karuwanci da caca
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta haramta duk wani ayyukan gidajen hala a jihar.
Hukumar Hisbah ta ce ta dauki matakin ne domin bin tsarin addini da kare kyawawan dabi’u a fadin jihar baki daya.

Asali: Original
An haramta karuwanci da caca a Katsina
Kwamandan hukumar, Aminu Usman (Abu Ammar), ne ya bayyana haka a wata sanarwa da aka fitar a Katsina, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A watan Yuli 2024, hukumar Hisbah ta haramta karuwanci da caca a fadin jihar domin inganta tarbiyya da kare al’umma daga mugayen dabi’u.
Ya umurci masu gidajen badala su rufe wuraren su domin hana aikata abubuwan da suka sabawa tarbiyya da kuma kare tsaron al’umma.
Hukumar Hisbah ta gargadi masu gidajen casu
“Hukumar ta gargaɗi masu karya doka da cewa za a dauki matakin hukunci a kansu, hukumomin tsaro na da alhakin tabbatar da bin wannan umarni.”
“Muna aiki don gina al’umma nagari tare da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar Katsina."
-.In ji kwamandan Hisbah
Ya ce hukumar Hisbah ta sanar da hukumomin tsaro, ciki har da Kwamishinan Tsaro na Jihar, domin tabbatar da cewa an aiwatar da umarnin.
Kwamandan ya ce mataki ya dace da kokarin Hisbah na tabbatar da cewa al’umma na rayuwa bisa tsarin addini da dabi’un gari, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Haduran tankar mai: Gwamnatin Tinubu ta haramtawa wasu tankoki hawa titunan kasar
“Hisbah na sa ido kan duk wanda ke da salo ko tara gashi maras kyau, kuma za a dauki matakin da ya dace a kansu."
- In ji wata sanarwa
Hisbah ta kwace tulin kwamandan barasa a Katsina
Kun ji cewa Hukumar Hisbah a jihar Katsina ta samu nasarar ƙwace barasar da aka yi niyyar shigar da ita zuwa ƙaramar hukumar Daura.
Hisbah ta ƙwace barasar wacce ta kai kimanin katan 142 a yayin wani aikin sintiri domin kawar da munanan ɗabiu da rashin ɗa'a.
Asali: Legit.ng