Amurka Ta Yi Baki Biyu, Ta Musanta Zargin Dan Majalisa kan Daukar Nauyin Boko Haram
- Jakadan Amurka, Richard Mills Jr, ya ce babu wata hujja da ke nuna cewa USAID ta ba da tallafi ga Boko Haram kamar yadda ake zargi
- Dan majalisar Amurka, Scott Perry ne ya bayyana cewa hukumar ba da tallafin ta shahara wajen daukar nauyin ta'addanci a kasashe kamar Najeriya
- A martaninsa, Mista Mills ya nemi duk wanda yake da wata shaida a kan zargin USAID da Boko Haram da ya gabatar da ita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja — Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills Jr, ya ce babu wata hujja da ke tabbatar da zargin cewa Hukumar Raya Kasashe ta Duniya ta Amurka (USAID) ta ba da tallafi ga kungiyar Boko Haram a nan.
Mills ya bayyana hakan ne yayin da yake tattaunawa da manema labarai jim kadan bayan gabatar da jawabi a taron Gwamnonin Najeriya (NGF) da aka gudanar a daren Laraba a birnin Abuja.

Asali: Facebook
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Mills ya ce tun shekarar 2013 aka sanya Boko Haram a matsayin wata kungiyar ta’addanci ta kasashen waje.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce an kuma tabbatar da cewa an kafa tsauraran hanyoyin sa ido don tabbatar da cewa tallafin da Amurka ke bayarwa yana isa ga wadanda ake nufi da su.
Amurka ta barranta USAID da Boko Haram
Jaridar PM News ta ruwaito cewa Richard Mills Jr ya kalubalanci duk wanda ke da wata hujja da ke nuna an karkatar da kudaden USAID zuwa Boko Haram da ya gabatar da ita.
Mills ya jaddada aniyar Amurka na ci gaba da taimakawa Najeriya wajen yakar ta’addancin Boko Haram, yana mai cewa za a gudanar da cikakken bincike tare da hadin gwiwar hukumomin Najeriya.

Kara karanta wannan
Haduran tankar mai: Gwamnatin Tinubu ta haramtawa wasu tankoki hawa titunan kasar
Ya ce:
“Babu wata kawar Najeriya da ta fi Amurka nuna adawa da cin zarafin dan Adam da Boko Haram ke aikatawa.
“Tun daga shekarar 2013 muka sanya Boko Haram a jerin kungiyoyin ta’addanci na kasashen waje, domin hana kungiyar yin duk wani harkar hada-hadar kudi da Amurka.”
Amurka ta ci alwashin taimakon Najeriya
Jakadan Amurka ya ce matakan da Amurka ta dauka ya ba ta damar kama da kuma kwace dukiyoyin da ke da alaka da Boko Haram, tare da jaddada goyon baya ga bincike da gwamnatin Najeriya ke yi.
Mista Mills ya ce:
“Ina tabbatar muku da cewa muna da tsare-tsare da ka’idoji da ke tabbatar da cewa kudaden USAID ko na Ma’aikatar Tsaron Amurka ba su karkata zuwa hannun ‘yan ta’adda kamar Boko Haram ba.
“Babu wata hujja da na gani da ke tabbatar da hakan. Kuma idan har wani ya gabatar mana da wata shaida da ke nuna cewa wani shiri na tallafi yana tafiya hannun Boko Haram, nan take za mu fara bincike tare da hadin gwiwar hukumomin Najeriya.
"Amurka na tare da Najeriya," Mills
Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills ya bayyana cewa Amurka ba ta yanke tallafin da take bai wa Najeriya ba, sai dai ta dakatar da shi na tsawon kwanaki 90.
Ya sake nanata cewa suna tare da kasar nan wajen tabbatar da ta yaki 'yan ta'adda da ta'addanci a fadin Najeriya.
Ya ce:
“Na so in fayyace cewa dangane da Boko Haram, Amurka tana tare da Najeriya wajen ganin an kawar da wannan masifar kungiyar."
USAID: Majalisa ta gayyaci shugabannin tsaro
A baya, mun wallafa cewa Majalisar Dattawa ta dauki matakin sanin hakikanin gaskiya kan zargin cewa Hukumar Raya Kasashe ta Duniya ta Amurka (USAID) tana ba da tallafi ga kungiyar Boko Haram.
Saboda haka, majalisar ta bukaci mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, da shugabannin Hukumar Binciken Sirri ta Najeriya (NIA) da Hukumar Binciken Sojoji (DIA) don ba da bayani
Asali: Legit.ng