Najeriya za Ta Ci Kuɗin Kirifto, Gwamnati Ta Sake Maka Binance a Gaban Kotu
- Gwamnati ta shigar da ƙarar dala biliyan 81 a kan Binance bayan zarge-zargen da suka haɗa da jawo wa Najeriya asarar mai yawa
- Daga cikin hukumomin ƙasar dake tuhumar Binance da aikata laifuffuka da dama, akwai hukumar tattara haraji ta da hukumar EFCC
- Hukumar tattara kudaden haraji na zargin Binance da rashin yin rajista da kuma ƙetare dokokin haraji, da ƙin biyan wasu maƙudan haraji
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Gwamnatin Najeriya ta shigar da sabon ƙara a kan Binance Holdings Limited a Babbar Kotun Tarayya ta na neman diyyar Dala biliyan 81.
Gwamnatin na iƙirarin a biya ta wannan kuɗi ne bisa zargin Binance ta haddasa mata asarar tattalin arziki da kuma ƙin biyan haraji.

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Hukumar Kula da Haraji ta Tarayya (FIRS) ta ce ta shigar da ƙarar da aka sanya wa lamba FHC/ABJ/CS/1444/2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta na neman a biya tarar dala biliyan 79 saboda asarar tattalin arziki, dala biliyan biyu na bashin haraji, da Naira miliyan 231 a matsayin diyya ga Najeriya bisa ayyukan Binance.
Koken gwamnati a kan Binance
FIRS ta kuma zargi Binance da wasu manyan jami’anta biyu, Tigran Gambaryan da Nadeem Anjarwalla, da jawo wa Najeriya asara ta hanyar ƙin yin rajistar ayyukan kamfanin. Ita ma Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa, (EFCC) na gurfanar da Gambaryan da Nadeem a kan tuhuma guda biyar da suka shafi zargin safarar kuɗi.
Ana zargin Binance da ƙin biyan haraji
Sauran tuhume-tuhumen sun haɗa da ƙin biyan haraji da kuma take dokokin harkokin musayar kuɗin da take gudanar a ƙasar nan.

Kara karanta wannan
Cacar baki ta balle tsakanin APC, NNPP kan yi wa gwamnatin Abba Gida Gida kishiya
FIRS ta zargi Binance da ƙin biyan harajin kuɗin shiga na 2022 da 2023, wanda ya sa ta nemi a biya tarar 10% don cike giɓin kuɗin da Najeriya ta rasa.
Haka kuma ana son kamfanin na Binance da ya biya ribar 26.75% bisa tanadin kuɗin rance na Babban Bankin Najeriya (CBN).
Najeriya ta na bude sabon shafin shari'a da kamfanin ne a daidai lokacin da shugaban Binance, Tigran Gambaryan ke zargin jami'an gwamnatin ƙasar da neman na goro.
Dan majalisa ya shigar da ƙarar Binance
A wani labarin, mun ruwaito cewa dan majalisar wakilai, Philip Agbese, ya shigar da kara a Babbar Kotun Birnin Tarayya da ke Abuja, inda yake zargin shugaban kamfanin Binance, Tigran Gambaryan, da bata masa suna.
Wannan ya biyo bayan zargin da Gambaryan ya yi na cewa Agbese da wasu 'yan majalisa biyu sun nemi cin hancin miliyoyin Daloli, lamarin da dan majalisar ya bayyana a matsayin sharri da kokarin zubar masa da mutunci.
Ɗan majalisar ya ce wannan mawuyacin hali da aka saka shi ya sa shi tafiya kotu, yana neman diyya ta naira biliyan daya daga Gambaryan, tare da naira miliyan biyar a matsayin kudin shari'a.
Asali: Legit.ng