Adamawa: An Shiga Fargaba da Bindiga Ta Tashi a Wurin Ibada, Mutane Sun Jikkata
- Wani mafarauci ya harba bindiga ba da gangan ba yayin taron cocin LCCN a Demsa da ke jihar Adamawa a Arewacin Najeriya
- Lamarin da ya faru ya yi sanadin raunata akalla mutane takwas yayin da aka kai su asibiti suna karbar kulawa domin tabbatar da ba su kulawa
- ‘Yan sanda sun kama mafaraucin yayin da Kwamishinan ‘yan sanda ya gargadi masu tsaron irin haka kan daukar bindiga wurin taruka
- An bukaci mazauna Demsa su taimaka wa ‘yan sanda don gujewa irin wannan hatsari a nan gaba, domin tabbatar da zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Demsa, Adamawa - A kalla mutane takwas ne suka jikkata bayan da bindigar wani mafarauci ta tashi bisa kuskure.
Lamarin ya faru ne yayin yayin babban taron cocin LCCN a karamar hukumar Demsa da ke Adamawa da ke Arewacin Najeriya.

Asali: Original
Bindigar ta yi sanadin raunata mutane 8
Mafaraucin dan kungiyar masu farauta ne daga Kukta a Song, yana dauke da bindigar toka domin tsaro a wurin taron, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin ‘yan sanda, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya ce bindigar ta subuce daga hannunsa, ta tashi sau da dama, lamarin da ya jikkata mutane.
Ya kara da cewa wadanda suka jikkata suna samun kulawa a asibiti da ke Demsa, kuma ana ci gaba da bincike kan lamarin domin kare faruwar hakan a gaba.
Yan sanda sun kama faraucin a Adamawa
Nguroje ya ce an kama mafaraucin amma ba za a bayyana sunansa ba har sai an kammala bincike kan abin da ya faru a wurin taron, cewar Daily Post.
Kwamishinan ‘yan sanda, Dankombo Morris, ya yi Allah-wadai da lamarin, yana mai gargadin masu tsaron gari kan amfani da bindiga a taruka.
Ya bukaci mazauna Demsa da su hada kai da ‘yan sanda domin gujewa irin wannan hatsari a nan gaba da kuma tabbatar da zaman lafiya.
Yan bindiga sun kai hari a asibitin Adamawa
Kun ji cewa Rundunar 'yan sandan Adamawa ta tabbatar da cewa wasu masu garkuwa da mutane sun sace akalla mutane hudu a jihar.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Suleiman Nguroje ya tabbatar da kai harin da aka kai asibitin koyarwa na Maodibbo.
Lamarin ya faru ne a kauyen Mayo Kila, wani yanki da ke kusa da iyakar Najeriya da Kamaru a karamar hukumar Jada ta Jihar Adamawa.
Asali: Legit.ng