'Ku Tuna Ramadan Ya Kusa': Yan Kasuwar Kano Sun Roki Dangote, Mai Kamfanin BUA

'Ku Tuna Ramadan Ya Kusa': Yan Kasuwar Kano Sun Roki Dangote, Mai Kamfanin BUA

  • Kungiyar ‘yan kasuwa a Kano ta roƙi kamfanonin Dangote da Bua su rage farashin sukari kafin Ramadan don rage wa talakawa wahala
  • Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ya yaba wa gwamnati kan sauƙin farashin kayan masarufi, amma ya ce masu siyarwa na ƙin rage farashi
  • ‘Yan kasuwar sun bukaci gwamnati ta ba da damar shiga kasuwar sukari ga kamfanoni da dama don samar da gasa da rage farashi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Kungiyar ‘yan kasuwar 'Singer' Singer a Kano, ta bukaci kamfanonin Dangote da Bua su rage farashin sukari kafin Ramadan.

Yan kasuwar suka ce yin hakan zai taimaka ga talakawa musamman yadda ake tunkarar azumin watan Ramadan.

An roki Dangote da BUA su rage farashin kaya kafin Azumi
Yan kasuwar 'Singer' sun roki Dangote da BUA su rage farashin kaya saboda Ramadan. Hoto: BUA Group, Dangote Foundation.
Asali: Facebook

Yan kasuwar Kano sun roki gwamnati alfarma

The Guardian ta ce ‘yan kasuwar sun roƙi gwamnati da ta bai wa kamfanoni da dama damar shiga kasuwar abinci domin samar da gasa da rage farashi.

Kara karanta wannan

Ana shirin fara azumi, gwamnati ta yi magana kan rage farashin kayan abinci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yawan kamfanoni a kasuwar abinci zai taimaka wajen rage farashin kayan masarufi, wanda hakan zai ba masu siyan kaya sauƙi.

Da yake jawabi, shugaban kungiyar ‘yan kasuwa, Junaidu Muhammed Zakari, ya ce Aliko Dangote da BUA na da nauyin rage wa jama’a wahala.

Yadda farashin kaya ya sauko a kasuwanni

Duk da cewa farashin shinkafa, gari, madara, wake da taliya sun ragu a Kano bayan sassaucin da gwamnati ta bayar, har yanzu sugar na da tsada.

Shugaban kasuwar ya ce duk da sauƙin farashin kaya, masu siyarwa na ƙin rage farashi, wanda ke hana masu amfani jin daɗin sauƙin da ake samu.

Ya yi nuni da irin wannan matsala a farashin burodi, inda ya ce duk da raguwar farashin gari, masu yin burodi sun ƙi rage farashi.

Zakari ya bukaci gwamnati ta ƙara kokari wajen inganta tsaro domin manoma su samu damar noma ba tare da fargaba ba, wanda hakan zai ƙara yawan abinci.

Kara karanta wannan

Rumbun sauki: Gwamna ya bude wuraren sayar da abinci da araha ga talakawa

"Muna yaba wa gwamnati kan sassaucin shigo da shinkafa, taliya wanda ya sa farashinsu ya ragu sosai a kasuwa.
"Misali, shinkafa da ake sayarwa N120,000 a baya yanzu ta ragu zuwa kasa da N80,000, yayin da taliya ta ragu daga N20,000 zuwa N13,500."
"Haka nan gari da ake sayar da shi N90,000, yanzu yana tsakanin N65,000 zuwa N70,000, yayin da man girki daga kusan N100,000 ya koma N70,000."
"Amma abin mamaki, ba a samu sauƙi a farashin sugar ba, shi ya sa muke roƙon gwamnati ta ƙara gasa a kasuwar sukari."
"Ya kamata a bada dama ga kamfanoni da yawa su shiga kasuwar sukari, me yasa sai kamfanoni biyu ko uku ke tafiyar da farashi?"

- Cewar Junaidu Zakari

Wani ɗan kasuwa ya tattauna da Legit Hausa

Dan kasuwa a Gombe, Alhaji Muhammad Auwal ya ce tabbas akwai bukatar samun saukin kaya daga manyan kamfanoni.

Ya ce:

"Ya kamata Dangote da mai kamfanin BUA su duba tsadar rayuwa da ake ciki domin saukakawa al'umma."

Kara karanta wannan

Muhimman dalilai 4 da suka karya farashin abinci ana shirin azumin Ramadan

Ya ce a yanzu komai ya dagule kowa na abinci kawai yake nema domin kai wa bakin salati.

Ya shawarci ƙananan yan kasuwa irinsa su rika tausayawa daidai gwargwado domin su ma su samu sauki.

Dangote ya magantu kan wahalar da ya sha

A baya, kun ji cewa fitaccen dan kasuwa, Aliko Dangote ya bayyana yadda ya fuskanci matsin lamba daga wasu mutane da ke kokarin hana nasarar matatar man fetur dinsa.

Attajirin ya ce da aikin matatar ya gaza kammaluwa, da shi kansa ya rasa komai a duniya, kasancewar ya saka jari mai yawa a aikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.