"Tinubu Mutumin Kirki ne, Yana da Niyya Mai Kyau," Babban Malami Ya Yi wa Mutane Nasiha
- Wani babban limamin coci a jihar Legas, Fasto Sam Olu Alo ya ce shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na da kyakkyawar niyya
- Malamin ya bukaci shugabannin addinai da ƴan Najeriya su daina zagin shugaban ƙasa, maimakon haka su dage da nema masa shiriya wurin Allah
- Faston ya kuma shawarci gwamnati ta ƙarfafa matasa su rungumi harkar noma, yana mai cewa ita ce hanyar bunƙasa tattalin arziki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Fitaccen malamin addini, Fasto Sam Olu Alo, ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da rokon Allah ya ba gwamnatin Shugaban ƙasa, Bola Tinubu nasara.
Babban limamin cocin ya jaddada cewa jagoranci na bukatar shiriya daga Allah, musamman a shekarar 2025.

Asali: Facebook
Ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi a wani taro da aka shirya a cocin Jesus City da ke kan titin Lekki-Epe a jihar Legas, kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu na bukatar goyon baya
Fasto Alo, wanda shi ne ya kafa cocin Christ Apostolic Church (CAC), ya bukaci ‘yan kasa su mara wa shugabanninsu baya ta hanyar addu’a, don neman hikima da basira daga Allah.
Limamin cocin ya ce:
“‘Ya kamata ƴan Najeriya su ci gaba da goyon bayan Shugaba Bola Tinubu tare yi masa addu’a. Shugaban kasa yana da kyakkyawar niyya; ba ya jin dadin halin kunci da ake ciki a kasar nan."
“Duk da halin da ake ciki, idan wadanda muka zaba sun fahimci dalilin da ya sa muka ba su amanarmu, akwai bukatar mu kuma mu ci gaba da yi musu addu’a.
"Ba kowa ne ya amince da manufofin Awolowo ba, da ace duk ‘yan kasa sun goyi bayansa, da ya zama shugaban ƙasa. Amma bayan mutuwarsa mutane sun gane darajarsa.”
Mutane su nema wa shugabanni shiriya
Fasto Alo ya jaddada muhimmancin yin addu’a domin nasarar Shugaba Tinubu, yana mai cewa hakan zai sa Allah ya shiga lamarinsa kuma ya taimaka masa.
“Shugabanni da aka zaba su fahimci cewa matsayin da suke kai ba hakkinsu ba ne, dama ce da suka samu. Akwai mutane da yawa da suka fi su cancanta amma ba su samu wannan dama ba.”
Malami ya bukaci a daina zagin Tinubu
Ya kuma bukaci malaman addini a faɗin Najeriya su yi wa gwamnati addu’a maimakon zagin shugabanni.
“Dole ne mu daina zagin shugabanni, mu rika ba su shawara. Ya kamata mu rika fadin abubuwa masu kyau game da kasarmu kamar yadda ‘yan kasashen da suka ci gaba ke yi.”
Sam Olu Alo ya kuma bukaci gwamnati ta karfafa wa matasa gwiwa su koma harkar noma, yana mai cewa noma na da matukar muhimmanci wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.
Tinubu ba zai kai labari ba a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa malamin addinin Musulunci, Sheikh Murtala Asada zai wahala shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi tazarce a 2027.
Malamin ya bayyaɓa cewa yadda shugaban ya illata Arewacin Najeriya kaɗai zai zama sanadin faɗuwarsa a zaɓe mai zuwa.
Asali: Legit.ng