Malamai Sun Yi Hukunci a Rikicin Kundila, Bin Usman zai Koma Tsohon Masallaci

Malamai Sun Yi Hukunci a Rikicin Kundila, Bin Usman zai Koma Tsohon Masallaci

  • Majalisar Malamai ta Kano ta warware rikicin masallaci da ake tsakanin Sheikh Muhammad Bin Usman da 'yan kwamiti a Kundila
  • Hukuncin da aka yanke shi ne Sheikh Muhammad Bin Usman zai ci gaba da jagorantar salla a Masallacin Sahaba bayan barin Jami’urrahma
  • Sheikh Muhammad Bin Usman Kano ya sanar da lokaci da ranar fara jagorantar sallar Jumu’a a Masallacin Sahaba da ya bari a baya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Majalisar Malaman jihar Kano ta bayyana hukuncin karshe dangane da rikicin da ya ɓarke da Sheikh Muhammad Bin Usman a masallacin Jami’urrahma.

Shugaban majalisar, Sheikh Ibrahim Khalil, ya bayyana cewa bayan nazari da tattaunawa da dukkan bangarorin da abin ya shafa, an cimma matsaya da za ta tabbatar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

An kusa shan jar miyan Pi, dan majalisa ya maka shugaban Binance a gaban kotu

Bin Usman
Sheikh Bin Usman zai koma tsohon masallacinsa a Kano. Hoto: Shaykh Muhammad Bin Uthman
Asali: Facebook

An wallafa a shafin Muhammad Bin Usman na Facebook cewa zai koma jagorantar sallah a masallacin Sahaba na Kundila.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sheikh Muhammad Bin Usman zai cigaba da jagorantar sallah a Masallacin Sahaba, yayin da wani limami zai cigaba da jagorantar salla a Masallacin Jami’urrahma da ke Shika a Kundila.

Sabanin da aka samu a kan Kundila

Legit ta rahoto cewa an fara rikicin a masallacin ne yayin da Sheikh Bin Usman ya ce an zalunce shi a wata huduba da ya yi.

Wani attajiri, Alhaji Ado Yahaya Mai Kifi ya gina katafaren masallaci a Kundila inda aka sanya Bin Usman cikin limamai kuma aka bukaci ya ajiye limanci a tsohon masallacinsa na Sahaba.

Daga baya Sheikh Bin Usman ya koka kan cewa ba a ba shi cikakken iko ba a kan sabon masallacin Jami’urrahma, lamarin da ya kai ga dakatar da shi.

Majalisar malaman Kano ta shiga lamarin inda ta zauna domin warware sabanin da aka samu a tsakanin malaman.

Kara karanta wannan

'Abin ya yi muni': An kashe mutane 6 da magoya bayan APC, PDP suka kacame da fada

Hukuncin da majalisar malamai ta yanke

Majalisar malaman Kano ta yanke hukunci da cewa Sheikh Muhammad Bin Usman zai koma tsohon masallacinsa na Sahaba.

Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana cewa an dauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya da kawo karshen ce-ce-ku-ce da ya dabaibaye rikicin masallacin.

Farfesa Salisu Shehu
Farfesa Salisu Shehu, daya daga cikin masu limanci a masallacin Jami'urrahma. Hoto: Anas Musa Fagge
Asali: Facebook

Malamin ya ce:

"Bayan zaman da muka yi da bangarorin da ke da sabani, mun cimma matsaya cewa Sheikh Muhammad Bin Usman zai cigaba da jagorantar sallah a Masallacin Sahaba."

Sheikh Khalil ya kara da cewa majalisar ta dauki matakin ne bisa adalci da hangen nesa domin dakile rikici a tsakanin al’ummar Musulmi a Kano.

Bin Usman zai jagoranci sallar Jumu’a

Bayan yanke hukuncin, Sheikh Muhammad Bin Usman ya tabbatar da cewa zai cigaba da jagorantar sallah a Masallacin Sahaba, kuma ya sanar da lokacin da zai gudanar da sallar.

Malamin zai jagoranci sallar Jumu’a a Masallacin Sahaba a ranar Jumu’a, 21 ga watan Fabrairu, 2025.

Kara karanta wannan

Rundunar sojoji ta yi magana kan zargin jefawa bayin Allah bam a jihar Katsina

An ruwaito cewa za a fara huduba da karfe 12:30 na rana, sannan za a tsayar da sallah da karfe 1:00 na rana.

Malamin Kano ya shiga APC a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa wani malamin Darikar Qadiriyya ya shiga siyasa ta hannun Sanata Barau Jibrin a Abuja.

Malamin ya jagoranci magoya bayansa zuwa APC a Abuja inda mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya tarbe su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng