Duk da Kisan Shugaban Karamar Hukuma, Ciyamomin APC Sun Yi Bajinta, Sun Koma Ofis

Duk da Kisan Shugaban Karamar Hukuma, Ciyamomin APC Sun Yi Bajinta, Sun Koma Ofis

  • Shugabannin APC na kananan hukumomi da kansiloli a Osun sun koma ofis a kananan hukumomi 14, tare da rakiyar magoya baya
  • Tsohon hadimin gwamna, Jami’u Olawumi ya ce jami’an tsaro sun kasance a yankunan da shugabannin APC suka koma
  • Ya bukaci Gwamna Adeleke ya tuntubi Shugaban kasa da IGP don tabbatar da cewa an aiwatar da hukuncin da ke ba APC damar ci gaba da mulki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Rahotanni sun tabbatar da cewa shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da aka zaba a zaben 15 ga Oktoba, 2022, sun koma ofis a jihar Osun.

Shugabannin sun koma ofisoshinsu ne duk da rigimar da ta barke wanda ya yi ajalin wani shugaban karamar hukuma.

Ciyamomin kananan hukumomi sun koma ofis duk da rigimar da ta barke
Shugabannin kananan hukumomi sun koma ofis bayan rigimar da ta jawo asarar rayuka. Hoto: Ademola Adeleke.
Asali: Twitter

Ciyamomi sun koma ofis bayan rasa rayuka

Kara karanta wannan

DSS ta gano makamai a ofishin hadimin tsohon shugaban majalisar Legas

Binciken The Punch ya nuna cewa shugabannin APC sun koma ofis tare da magoya bayansu a Ila da Ede ta Kudu da Ife ta Tsakiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai kuma Ife ta Gabas da Ife ta Arewa da Ilesa ta Gabas da Ilesa ta Yamma da Boripe da Oriade da kuma Obokun da Ejigbo, Iwo, Ayedire da Boripe.

Yayin da yake tsokaci, tsohon mai ba gwamna shawara kan ilimi, Jamiu Olawumi, ya ce shugabannin sun koma ofis a kananan hukumomi 14 da misalin karfe 10 na safe.

An yabawa Gwamna kan samar da tsaro

“Muna da 14 daga karfe, Jami’an rundunar ‘yan sanda, Civil Defence da DSS suna nan a harabar sakatariyar."
“Muna yabawa Gwamna Adeleke, amma hakan kadai bai isa ba, ya kamata su cire ’yan daba da suka kawo nan.
"Idan ka zagaya gari, za ka ga fuskoki da ba ka saba gani ba, bai kamata a bar ’yan daba su cutar da al’ummar Osun ba."

Kara karanta wannan

Ana fargabar tsohon ciyaman ya bace bayan mummunan harin yan bindiga a Kebbi

“Sun fahimci cewa hukuncin yana da karfi. Gwamnan ya tuntubi Shugaban kasa, Shugaban Ma’aikatan fadar shugaban kasa ko Sufeto Janar na ‘yan sanda, ya kamata ya yi hakan don ganin an cimma burin bunkasa Osun a wa’adinsa.
“Shugabanninmu da kansiloli a shirye suke su yi aiki da shi, ko da yake suna daban da gwamnatinsa."

- In ji Olawumi

An hallaka shugaban karamar hukuma a Osun

Kun ji cewa Ana zargin 'yan bangar siyasar PDP ne sun kashe Mista Remi Abass, shugaban karamar hukumar Irewole da ke a jihar Osun.

APC da PDP na jayayya kan iko da karamar hukumar, inda APC ta ce kotun daukaka kara ta dawo da shugabannin da aka sallama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.