DSS Ta Gano Makamai a Ofishin Hadimin Tsohon Shugaban Majalisar Legas

DSS Ta Gano Makamai a Ofishin Hadimin Tsohon Shugaban Majalisar Legas

  • Jami'an hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun samu manyan bindigu da alburusai a ofishin jami'in tsaron tubabben shugaban majalisar jihar Legas
  • 'Yan majalisar sun raba Mudashiru Obasa da mukaminsa bisa wasu dalilai, lamarin da ya ke ikirarin an yi shi ba bisa tanadin dokar kasa ba
  • Makusantan tsohon shugaban sun bayyana cewa akwai zargin cewa gano manyan makaman da aka yi sharri ne a kokarin batawa Obasa suna
  • Zuwa yanzu, babu wani martani a hukumance daga Rt. Hon Obasa ko kuma hukumar tsaron ta DSS a kan gano miyagun makaman ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Jami’an Hukumar Tsaro ta DSS sun gano wasu manyan bindigu a ofishin jami’in tsaron tsohon shugaban majalisar dokokin jihar, Mudashiru Obasa, wanda aka tube daga mukaminsa.

Kara karanta wannan

An kusa shan jar miyan Pi, dan majalisa ya maka shugaban Binance a gaban kotu

Wani dan majalisar ya bayyana cewa an gano bindigogin ne a lokacin da jami'an tsaron ke gudanar da aikin bincike, inda aka ci karo da wasu alburusai a ofishin.

Obasa
Ana zargin hadimin Obasa da ajiye miyagun makamai Hoto: Hon. Mudashiru Obasa
Asali: Facebook

A labarin da ya kebanta ga The Cable, wani makusancin shugaban majalisar ya bayyana cewa wannan batu wani yunkuri ne na bata masa suna tare da hana shi dawowa kujerarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legas: Obasa ya ki amincewa da tsige shi

Mudashiru Obasa ya dage kan cewa tube shi daga mukamin shugaban majalisar ba bisa ka’ida aka yi ba, kuma har yanzu shi ne mutum na uku mafi daraja a jihar.

Duk da haka, wata majiya ya bayyana cewa:

“Jami’an majalisa sun gano wasu bindigogi da aka aje a ofishin jami’in tsaron Obasa. Nan take suka sanar da DSS, inda suka turo jami’ansu don tattara bayanai kan makaman, sannan suka kwashe su don bincike.”

Legas: Shugaban majalisa na fafutukar komawa ofis

Ana ta rade-radi da dama game da gano makamai a ofishin hadimin Obasa, har ma wasu suna zargin yana da alaka da safarar makamai saboda yawan kayan da aka samu.

Kara karanta wannan

An gano dalilin faduwar farashi a shahararriyar kasuwar abinci a Kano

Wani dan majalisa ya bayyana cewa Obasa na “yin duk mai yiwuwa don komawa ofis dinsa” domin bayan 'yan majalisa sun bijirewa jagorancinsa.

Ya kara da cewa:

Yanzu DSS da hukumomin tsaro za su gudanar da nasu aikin. Idan aka boye wannan batu, Legas da ma Najeriya za su gane inda matsalar take.”
“Lokacin da muka shaida wa jama’a cewa majalisa ta gaji da Obasa, mutane ba su fahimci abin sosai ba.”

Dalilan tsige shugaban majalisar Legas

A wani labarin, mun ruwaito cewa 'yan majalisar dokokin jihar Legas sun tsige Mudashiru Obasa daga mukaminsa na Kakakin Majalisar, wanda ya shafe shekaru 10 yana rike da kujerar.

Majalisar ta bayyana cewa daga cikin dalilan tsige shi akwai rashin zuwa taro da zaman majalisar a kan lokaci, tare da yawan yin biris da ra’ayoyin sauran ‘yan majalisar.

Bayan tsige Obasa bisa zargin kokarin hada membobin majalisa fada da junansu, ‘yan majalisar sun nada tsohuwar mataimakiyarsa, Mojisola Lasbat Meranda, a matsayin sabon shugaban Majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.