Ana Shirin Fara Azumi, Gwamnati Ta Yi Magana kan Rage Farashin Kayan Abinci
- Gwamnatin tarayya ta bukaci ‘yan kasuwa su rage farashin kayan abinci, musamman kan kayan bukatu irin su shinkafa da fulawa
- Ministan noma, Abubakar Kyari ya nuna damuwa kan yadda 'yan kasuwar suka ki rage farashi duk da farashin kayan masarufi ya sauka
- Gwamnati ta tallafa wa manoman Jigawa da kayan aikin noma na biliyoyin naira, ciki har da injinan ban ruwa, feshi, da takin zamani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jigawa - Gwamnatin Tarayya ta bukaci ‘yan kasuwa da masu sayar da kayan abinci da su rage farashi bayan faduwar farashin kayan masarufi a kasuwa.
Ministan noma da tsaron abinci, Abubakar Kyari, ya yi wannan kiran ne a bikin ranar manoman alkalama ta 2025 da aka shirya a karamar hukumar Ringim, jihar Jigawa.

Source: Getty Images
Gwamnati ta nemi a rage farashin kayan abinci
A cewarsa, gwamnati ta fahimci cewa, duk da cewa farashin wasu kayan abinci ya ragu, har yanzu masu sayar da kayan masarufi ba su rage farashin su ba, inji rahoton Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kyari ya ce farashin abinci ya ragu sosai a kasuwanni, musamman kayan bukatu irin su fulawa, sukari, shinkafa da taliya.
A da, buhun fulawa ya na kan N81,000 amma yanzu ya dawo kasa da N60,000, yayin da farashin taliya ya ragu daga N20,000 zuwa N15,000.
Sai dai ya nuna damuwa cewa yawancin ‘yan kasuwa da masu sayar da kayan abinci ba su rage farashin kayan su ba, lamarin da ke hana ‘yan Najeriya samun sauki.
Gwamnati ta ba manoman Jigawa tallafi
Ya bukaci dukkan ‘yan kasuwa da masu sayar da kayan abinci da su daidaita farashin su da yanayin kasuwa na yanzu domin rage wa jama’a radadin tsadar rayuwa.
Bugu da kari, ministan ya sanar da bayar da tallafin N5bn ga manoman jihar Jigawa don inganta harkokin noma da bunkasa samar da abinci.
Tallafin ya haɗa da injinan ban ruwa 10,000, injinan feshi 10,000, da takin zamani domin taimakawa manoma wajen inganta girbin su.
Gwamnatin tarayya ta ce tana kokarin tabbatar da wadatar abinci da kuma rage farashi domin saukaka matsin tattalin arziki da ake fuskanta a kasar.
Masana gabatar da bukatu ga gwamnati
Wasu masana harkar noma sun bukaci gwamnati da ta kara inganta hanyoyin sadarwa tsakanin gwamnati da manoma domin a samu daidaiton farashi a kasuwa.
Sun ce, idan gwamnati ta samar da hanyoyin rarraba abinci kai tsaye ga masu saye, hakan zai hana dillalai kara farashi ba gaira ba dalili.
Har ila yau, wasu ‘yan kasuwa sun bukaci a samar da karin tallafi ga masu sarrafa abinci domin rage tsadar samar da kayayyakin masarufi.
Jihar Arewa da ake sayar da abinci a araha
A wani labarin, mun ruwaito cewa, farashin kayan hatsi ya fadi a kasuwar Dandume da ke a jihar Katsina, ranar Laraba, 22 ga Janairu, 2025.
Farashin shinkafa ya sauko zuwa N55,000, yayin da wake, gero, da dawa suma suka fadi kasa a kasuwa.
Sabbin farashin buhunan hatsi sun hada da masara N50,000-N55,000, dawa N50,000-N56,000, gero N67,000-N70,000, da waken soya N70,000-N78,000.
Asali: Legit.ng

