An Shiga Tashin Hankali a Abuja: 'Yan Bindiga Sun Kashe Wasu Mutane da Suka Sace

An Shiga Tashin Hankali a Abuja: 'Yan Bindiga Sun Kashe Wasu Mutane da Suka Sace

  • ‘Yan bindiga sun kashe wasu matasa biyu da suka yi garkuwa da su a Gwargwada, Kuje da ke Abuja, saboda jinkirin biyan kudin fansa
  • Masu garkuwar sun bukaci N1m kudin fansa, amma iyalan samarin suka tara N500,000 kacal, wanda aka ce ya jawo aka kashe samarin
  • Sarkin Gwargwada ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa har yanzu ba a samu gawarwakin samarin ba amma ana kan bincike

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - ‘Yan bindiga sun kashe mutum biyu da suka sace a kauyen Gwargwada, yankin Kuje na Abuja, sakamakon jinkirin biyan kudin fansa.

An sace wadanda aka kashe, Mohammed Danladi da Nasiru Yusuf, tare da wani makiyayi da wata mata a kan hanyar Gwargwada-Rubochi, kusa da shatale-talen Gwombe , a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun dakile shirin masu garkuwa da mutane, sun cafke miyagun masu laifi

Basarake ya yi magana da 'yan bindiga suka kashe wasu mazauna Abuja
'Yan bindiga sun kashe wasu mazauna Abuja saboda an yi jinkirin kai kudin fansarsu. Hoto: @FCT_PoliceNG
Asali: Facebook

An kashe matasan da aka sace a Abuja

Shuaibu Abdullahi, dan uwan mamatan, ya ce masu garkuwa sun nemi N500,000 daga kowannensu, amma iyalan sun iya hada N500,000 kacal, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, a ranar Juma’a, shugaban 'yan bindigar ya kira yana bukatar kudin fansa, ba tare da iyalan sun san cewa an riga sun kashe mutanen biyu saboda jinkirin biya ba.

Bayan karɓar Naira miliyan uku, ‘yan bindigar sun sako makiyayin da matar da suka sace a maboyarsu da ke dajin Kotonkarfe, Jihar Kogi.

Basarake ya yi karin haske kan abin da ya faru

'Yan bindiga sun kashe matasa a Nasarawa
'Yan bindiga sun kashe matasa a Nasarawa, har yanzu ba a ga gawarsu ba. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Sarkin Gwargwada, Ugbada Alhaji Hussaini Agabi Mam, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an sace matasan ne a hanyarsu ta dawowa daga Rubochi.

Alhaji Hussaini ya ce:

"Abin takaici ne yadda suka kashe wadannan samari biyu saboda kawai kudin fansa bai iso wajensu da wuri ba."

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ga ta kansa: An jero manyan ƴan siyasa 17 da suka fice daga jam'iyyar LP

Ya kara da cewa har yanzu ba a samu gawarwakin mutanen ba, amma shugaban karamar hukumar Kotonkarfe ya tura ‘yan sa-kai da mafarauta domin bincike a dajin.

"Ba a samu gawarwakinsu ba tukuna domin an dauke su zuwa dajin Kotonkarfe a Jihar Kogi. Amma na ji cewa shugaban Kotonkarfe ya tura mafarauta da ‘yan banga zuwa dajin, sai dai har yanzu ba a samo gawarwakin biyu ba."

- Alhaji Hussaini.

Har yanzu ba a samu wata sanarwa daga rundunar ‘yan sandan Abuja kan lamarin ba.

Duba wasu labaran kan hare-haren 'yan bindiga

'Yan bindiga sun kai hari jihar Filato, sun kashe mutane tare da sace wasu da dama

'Yan bindiga sun tare hanyar Tsafe zuwa Funtua, sun kashe matafiya tare da sace wasu

'Yan bindiga sun kashe shugaban makaranta da wasu mutane 7 a hanyar zuwa Wukari

'Yan bindiga sun kashe matasa a harin ta'addanci da suka kai ƙaramar hukumar Bokkos

Kara karanta wannan

'Ya aikata laifuffuka 5': An gurfanar da fitaccen mawakin Najeriya a gaban kotu

'Yan bindiga sun kashe dan malamin addini

A wani labarin, mun ruwaito cewa, ‘yan bindiga sun kashe ɗan faston cocin RCCG tare da sace matarsa, suna neman N30m a matsayin kudin fansa.

Faston Austin Ifeji ya tsira bayan an sare shi da adda, amma ‘yan bindigar sun kashe ɗansa yayin da yake kokarin kare mahaifiyarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.