Kisan Hafsah: 'Malamin Addinin Musulunci' Ya Shiga Matsala, An Tasa Ƙeyarsa Zuwa Gidan Yari
- Kotun majistire ta umarci a tsare Abdulrahmam Mohammed, wanda ya kira kansa da malamin addinin Musulunci a gidan gyaran hali
- Ana zargin malamin tare da wasu mutum huɗu da haɗa baki wajen kashe ɗalibar ajin karshe a kwalejin ilimi ta jihar Kwara, Hafsah Lawal
- Alkalin kotun ya umarci a garƙame waɗanda ake ƙara bayan sun amsa laifinsu kana ya ɗage ƙarar zuwa ranar 6 ga watan Maris
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kwara - Wata kotun majistare da ke zama a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, ta umarci a tsare wani matashi mai shekaru 29, Abdulrahman Mohammed Bello a gidan gyaran hali.
Kotun ta tura Abdulrahman, wanda ya yi ikirarin cewa shi malamin addinin musulunci ne, zuwa kurkuku bisa zargin kisan ɗaliba ƴar ahekara 24, Hafsah Lawal Yetunde.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa marigayyar, daliba ce da ke ajin ƙarshe a kwalejin ilimi ta jihar Kwara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa bayan kashe Hafsah, makasanta sun yi gunduwa-gunduwa da jikinta, lamarin da ya girgiza al'umma.
Me ya sa kotu ta tura malamin kurkuku?
An gurfanar da mai ikirarin malunta, Abdulrahman tare da wasu mutane hudu da ake zargi da hannu a lamarin.
Ana tuhumar su da laifuffukan da suka haɗa da haɗa baki wajen aikata laifi, kisan kai, fashi da makami da mallakar sassan jikin ɗan adam ba bisa ka'ida ba.
Wadanda aka gurfanar tare da malamin sun hada da Ahmed Abulwasiu, Sulaiman Muhydeen, Jamiu Uthman da AbdulRahman Jamiu, duk daga Ilọrin da Malete.
Bayani daga rahoton ‘yan sanda
A rahoton binciken farko na ‘yan sanda (FIR), Abdulrahman da sauran mutanen da ake zargi na cikin wata kungiyar asiri kuma sun amsa cewa sun aikata kisan ne domin yin tsafi.

Kara karanta wannan
Mutumin da Tinubu ya naɗa a muƙami ya tsallake rijiya da baya, an yi yunƙurin kashe shi
Lauyan gwamnati, Matthew Ologbonsaye, ya bukaci kotu da ta ci gaba da tsare wadanda ake zargi don ba wa ‘yan sanda damar ci gaba da bincike.
Mai shari’a Sanusi B. Mohamed bai iya sauraron karar gaba daya ba saboda kotun ba ta da hurumin sauraron irin wannan shari’a.
Ya umarci a tsare wadanda ake zargi a gidan gyaran hali na Oke Kura kana ya dage shari’ar har zuwa 6 ga Maris, 2025, kamar yadda Vanguard ta kawo.
Kotu ta ɗaure matashi kan laifin sata
A wani labarin, kun ji cewa kotun Musulunci a Kano ta ɗaure wani matashi ɗan shekara 20 a duniya, Murtala Halliru a gidan gyaran hali na tsawon watanni shida.
Matashin zak shafe waɗannan watanni a gidan gyaran hali ne bayan masa laifin satar da ake tuhumarsa, alkali ya umarci ya biya kudin kayan da ya sace.
Asali: Legit.ng