Rashawa da Cin Zarafin Ofis: 'Yan Majalisa Sun Taru, Sun Tsige Shugaban Alkalai

Rashawa da Cin Zarafin Ofis: 'Yan Majalisa Sun Taru, Sun Tsige Shugaban Alkalai

  • Majalisar dokokin Benue ta amince da tsige shugaban alkalan jihar, Maurice Ikpambese, bayan Gwamna Hyacinth Alia ya aike da wasika
  • Ana zargin Ikpambese da take dokokin aiki, karkatar da kudaden shari’a, goyon bayan yajin aiki, cin hanci da rashawa, da sauransu
  • Bayan tattaunawa mai zafi, ‘yan majalisa 23 daga cikin 31 sun kada kuri’ar amincewa da tsige alkalin alkalan jihar, Mai shari'a Maurice

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Benue - Majalisar dokokin jihar Benue ta amince da a gaggauta tsige babban alkalin jihar, Maurice Ikpambese, bisa zargin take dokokin aiki.

Yanke shawarar tsige shi ya biyo bayan wasikar da gwamna Hyacinth Alia ya aike wa majalisar, inda aka tattauna kan lamarin a zaman majalisa karkashin shugabancin kakakin majalisa, Hyacinth Dajoh.

'Yan majalisar Benue sun kada kuri'ar tsige shugaban alkalan jihar Benue.
Majalisar Benue ta amince a gaggauta tsige shugaban alkalan jihar. hoto: @BenueHouse (X)
Asali: Twitter

Ana zargin shugaban alakalai da rashawa

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun bankaɗo jihar da fitinannen ɗan ta'adda ya fake a Arewa

Gwamnan ya gabatar da zarge-zarge guda biyar da suka hada da zargin amfani da matsayi wajen sauya dokar zaben jihar da aka amince da ita, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kuma zarge shi da karkatar da kudaden da aka ware wa bangaren shari’a da kuma amfani da mukaminsa don cin gajiyar siyasa.

Sauran zarge-zargen sun hada da haddasa yajin aiki a bangaren shari’a da kuma aikata cin hanci da rashawa.

'Yan majalisa sun amince a tsige shugaban alkalai

A yayin zaman majalisar, shugaban masu rinjaye, Saater Tiseer, ya karanta wasikar gwamnan wacce ke dauke da bayanan tuhumar da ake yi wa babban alkalin.

Kakakin majalisar ya bukaci sakataren majalisa ya raba mambobi zuwa gida biyu bayan wasu ‘yan majalisa sun goyi bayan tsige alkalin, yayin da wasu suka ki amincewa.

The Nation ta rahoto cewa, ‘yan majalisa 23 daga cikin 31 ne suka kada kuri’ar amincewa da tsige Ikpambese daga mukaminsa.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke a majalisa, Akpabio ya fusata bayan umartar a yi waje da sanata

'Har yanzu Maurice ne shugaban alkalai" - NJC

Kungiyar NJC ta ce majalisar Benuwai ba ta bi dokokin mulkin Najeriya wajen dakatar da Maurice ba
Kungiyar NJC ta ce har yanzu Maurice ne shugaban alkalan Benuwai, ta gargadi majalisa. Hoto: @BenueHouse
Asali: Facebook

Hukumar Koli ta Shari'a (NJC) ta ce Mai Shari’a Maurice Ikpambese har yanzu shi ne Babban Alkalin Jihar Benue, inji rahoton Channels TV.

A cikin wata sanarwa da Kemi Ogedengbe ya sanya wa hannu, NJC ta ce Ikpambese zai ci gaba da rike mukamin har sai an kammala bincike.

Hukumar ta ce matakin da majalisar dokokin Benue ta dauka na tsige shi ba zai yi tasiri ba, tana mai cewa:

“Wannan lamari abin takaici ne, dokar 1999 ta Najeriya ta fayyace yadda ake nada da hukunta alkalan kotu. A cikin wannan batu, ba a bi sharuddan da kundin tsarin mulki ba.”

NJC ta ce ta karɓi ƙorafi kan Mai Shari’a Maurice Ikpambese amma har yanzu ba a fara bincike ba.

Hukumar ta jaddada cewa za a bi ka’idojin bincike da tabbatar da adalci kafin daukar mataki.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30

Majalisa ta soke dokar ba tsofaffin gwamnoni fansho

A wani labarin, mun ruwaito cewa, majalisar jihar Benue ta soke dokar da ke ba da damar ci gaba da kula da tsofaffin gwamnoni da mataimakansu.

Dokar ta tanadi biyan tsofaffin gwamnoni N25m, yayin da mataimakansu ke da hakkin karɓar N15m a matsayin fansho duk wata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.