Kwana Ya Ƙare: Dalibai 5 na Jami'ar Tarayya Sun Mutu Lokaci 1, an Dakatar da Karatu

Kwana Ya Ƙare: Dalibai 5 na Jami'ar Tarayya Sun Mutu Lokaci 1, an Dakatar da Karatu

  • Wata babbar mota ɗauke da manja da itace ta murƙushe ɗalibai biyar na Jami'ar Tarayya da ke Lokoja a jihar Kogi
  • Hukumar makarantar ta tabbatar da faruwar lamarin, ta dakatar da karatu domin jimami da alhinin rashin ɗaliban guda biyar
  • Mataimakin gwamnan jihar Kogi ya kai ziyarar jaje ga hukumar jami'ar kuma ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta ɗauki matakan kariya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Jami’ar Tarayya da ke Lokoja (FUL) a jihar Kogi ta shiga jimami bayan mummunan hadarin motar ya yi sanadin mutuwar dalibanta guda biyar.

Wata babbar motar dakon kaya ta markaɗe ɗaliban a yankin Felele da ke birnin Lokoja jiya Litinin, 17 ga watan Fabrairu, 2025.

Jami'r Tarayya da ke Lokoja.
Babbar Mota ta yi ajalin daliban Jami'ar Tarayya 5 a jihar Kogi Hoto: Federal University Lokoja
Asali: Facebook

Mataimakin Rajistara na jami’ar mai kula da harkokin hulɗa da jama'a, Vincent Ojo, ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar kuma aka wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Atiku ya zargi Tinubu da son sauya shugabancin majalisa da karfin mulki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Da zuciya mai cike da bakin ciki muke sanar da rasuwar ɗalibanmu biyar, waɗanda suka rasu sakamakon wani mummunan haɗarin motar da ya girgiza mu," in ji shi.

Yadda ɗaliban suka ransa ransu a haɗarin

Lamarin ya faru ne a ranar Litinin lokacin da wata babbar motar dakon kaya da ke dauke da manja da itacen girki ta danne motar bas da ɗaliban jami'ar ke ciki.

Babbar motar tana kan hanyar zuwa Abuja ne sa'ilin da ta latse bas da ɗaliban Jami'ar FUL ke ciki a Felele a Lokoja.

Jami'ar FUL ta ayyana shiga zaman makoki

Domin nuna alhini ga rasuwar daliban, jami’ar sun ta dakatar da dukkan darussa daga karfe 12 na rana a ranar Talata, 18 ga Fabrairu, kuma babu karatu a ranar Laraba, 19 ga Fabrairu, 2025.

"Mun taƙaita harkokin jami'ar sabida jimamin da ake cikin sannan za a sauke tutar makaranta zuwa rabi domin girmama ɗaliban da suka rasu," in ji Mista Ojo.

Kara karanta wannan

Rundunar sojoji ta yi magana kan zargin jefawa bayin Allah bam a jihar Katsina

Jami’ar ta kuma aike da sakon ta’aziyya da addu’o’i ga iyalan wadanda suka rasu, tare da rarrashin dalibai da malamai da ke cikin alhini da bakin ciki.

Gwamnatin Kogi ta kai ziyarar jaje

Bayan aukuwar wannan mummunar hadari, mataimakin gwamnan Kogi, Salifu Joel Oyibo, ya kai ziyara jami’ar domin yin ta’aziyya ga mahukunta da daliban jami’ar.

Ya tabbatar wa ɗaliban jami’ar cewa gwamnati za ta dauki matakai na gaggawa don magance hadurran da ke yawan faruwa a yankin Felele.

Wannan ba shi ne karon farko da hadura irin wannan ke faruwa a yankin, wanda ke da cunkoso na ababen hawa da manyan motocin dakon kaya ba.

Ƴan fashi sun kutsa ɗakin kwann ɗalibai

A wani labarin, kun ji cewa ƴan fashi da makami sun kutsa cikin jami'ar Ibadan da ke jihar Oyo, sun saci kayayyakin karatun ɗalibai.

An tattaro cewa ‘yan fashin sun yi awon gaba da wayoyi masu tsada, kayan ado, tufafi, da sauran kayayyaki masu daraja na ɗaliban kuma sun raunata wasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262