Gwamnonin Najeriya Sun Yi Jimami da Allah Ya Yi wa Manyan Dattawa 2 Rasuwa

Gwamnonin Najeriya Sun Yi Jimami da Allah Ya Yi wa Manyan Dattawa 2 Rasuwa

  • Gwamnoni jihohi 36 na Najeriya karkashin ƙungiyarsu ta NGF sun yi alhinin mutuwar dattawan kasa guda biyu, Cif Edwin Clark da Ayo Adebanjo
  • Shugabann NGF kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana cewa rasuwar mutanen 2 babban rashi ne ga ƙasa
  • Ya kuma miƙa sakon ta'aziyya ga al'ummar jihohin Delta da Ogun bisa rasuwar dattawan biyu tare da addu'ar samun salama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kwara - Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta bayyana jimami da alhininta kan rasuwar Ayo Adebanjo da Edwin Clark, waɗanda suka kasance manyan dattawan ƙasa kuma shahararrun ‘yan gwagwarmaya a Najeriya.

Shugaban kungiyar, kuma Gwamnan kihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ne ya miƙa sakon ta'aziyyar a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

Dattawan kasa.
Gwamnonin Najeriya sun yi ta'aziyyar rasuwar Edwin Clark da Adebanjo Hoto: @NGFSecretariat, James Ebiowou Manager
Asali: Facebook

Ya ce mutuwar wadannan dattawa babban rashi ne ga kasa, musamman duba da irin rawar da suka taka wajen ci gaban dimokuradiyya, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa sun yaba shirin Tinubu kan Arewa, sun tura muhimmin sako ga gwamnoni

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Najeriya ta yi rashin dattawa 2

Ayo Adebanjo, jagoran kungiyar al'adun Afenifere, ya rasu a ranar Jumma’a da ta gabata yana da shekaru 96 a duniya.

Marigayin ya kasance a sahun gaba wajen fafutukar kare muradun Yarbawa da kuma yaki da mulkin danniya a Najeriya.

Edwin Clark, wanda ya jagoranci kungiyar PANDEF ta Kudu maso Kudu, ya rasu a ranar Talata, 18 ga watan Fabrairu, 2025 yana da shekaru 97 a duniya.

Ya kasance fitaccen mai rajin kare hakkin ‘yan yankin Niger Delta, musamman batun raba arzikin kasa da kare hakkin al’ummomin yankin.

Gwamnoni 36 sun miƙa sakon ta'aziyya

Kungiyar gwamnonin jihohin Najeriya watau NGF ta mika sakon ta’aziyya ga al'ummar jihar Ogun da na jihar Delta, inda mamatan suka fito, tare da fatan Allah ya gafarta musu.

Kungiyar ta kuma bayyana cewa irin gudunmawar da suka bayar ga Najeriya ba za a manta da ita ba.

Kara karanta wannan

Mutumin da Tinubu ya naɗa a muƙami ya tsallake rijiya da baya, an yi yunƙurin kashe shi

NGF ta ƙara da cewa tarihi zai ci gaba da tunawa da su a matsayin shugabanni na gari da suka tsaya tsayin daka wajen kare haƙƙin al’umma da tabbatar da adalci.

Shugaba Tinubu ya yi alhinin mutuwar Clark

A wani labarin, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi alhinin mutuwar shugaban ƙungiyar al'ummar Kudu mado Kudu (PANDEF), Edwin Clark.

Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin mutum mara tsoro, wanda ya ba Najeriya gudummuwa mai dumbin yawa a zamanin rayuwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel