Sojoji Sun Dura Kan 'Yan Bindiga Suna Shirin Kulla Alaka da Boko Haram

Sojoji Sun Dura Kan 'Yan Bindiga Suna Shirin Kulla Alaka da Boko Haram

  • Dakarun sojoji sun kai farmaki kan sansanin ‘yan bindiga a dajin Sakkarawa, Sabon Birni, inda suka halaka da dama
  • Rahotanni sun nuna cewa wasu ‘yan bindiga ciki har da shugabansu sun tsere bayan sun sha raunuka sakamakon farmakin sojojin
  • Wani mutum da aka ceto daga hannun ‘yan bindiga ya bayyana yadda suke mu’amala da Boko Haram ta hanyar biyan kudin fansa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Dakarun sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar rundunar tsaro ta Operation Fansan Yamma tare da ‘yan sa-kai sun kai farmaki a sansanin ‘yan bindiga.

Rahotanni sun nuna cewa sojojin sun kai farmakin ne a dajin Sakkarawa da ke yammacin Sabon Birni na jihar Sokoto.

'Yan bindiga
Sojoji sun wargaza maboyar 'yan bindiga a Sokoto. Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Mai sharhi kan harkokin tsaro, Zagazola Makama ya wallafa a X cewa an halaka ‘yan bindiga da dama yayin da wasu suka tsere bayan sun samu raunuka.

Kara karanta wannan

'Yan banga sun yi jina jina ga 'yan bindiga da suka yi karon batta da dare

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bincike ya nuna cewa wannan sansani yana da matukar muhimmanci ga ‘yan ta’adda, kasancewarsa wajen taruwa da tsara hare-hare.

Sojoji sun rusa sansanin ‘yan bindiga

Bisa ga rahotannin sirri, sojoji sun gano sansanin ‘yan bindiga mai suna “Dabar Dan Dari Biyar” wanda ke dajin Sakkarawa.

A ranar 17 ga watan Fabrairu, 2025, dakarun sojoji da ‘yan sa-kai suka kai farmaki kan sansanin, inda suka halaka ‘yan bindiga da dama.

Wata majiya ta bayyana cewa wasu daga cikin shugabannin ‘yan bindigar sun tsere bayan sun gamu da mummunar hasara.

Harin ya kasance daya daga cikin manyan farmakin da aka kai kan sansanonin ‘yan ta’adda a yankin cikin ‘yan kwanakin nan.

Alakar 'yan bindiga da Boko Haram

Wani mutum da aka ceto daga hannun ‘yan bindiga ya bayyana irin wahalar da ya sha a hannunsu, inda ya kwashe watanni biyu yana tsare.

Kara karanta wannan

Sojoji sun raunata 'yan sanda yayin da suka daku da juna, an ladabtar da jami'ai

Ya ce ‘yan bindigar suna shirin mika wani kudin fansa har Naira miliyan 2 da kuma babur ga Boko Haram a ranar Alhamis mai zuwa.

Bayan hakan, ya bayyana cewa sansanin ‘yan bindigar yana da tsari na musamman, inda suka gina wuraren zama da gadon kwanciya.

Bayanan da mutumin ya bayar yanzu haka an mika su ga hukumomin tsaro domin daukar mataki na gaba.

Sojoji su bi sawun 'yan bindiga a Sokoto

Bayan kammala farmakin, sojoji sun fara bin sawun ‘yan bindigar da suka tsere domin su tabbatar sun kakkabe yankin gaba daya.

Jami’an tsaro sun yi alkawarin cewa ba za su yi kasa a guiwa ba har sai sun murkushe duk wata barazana daga ‘yan ta’adda.

Sojojin Najeriya sun bukaci jama’a su ci gaba da ba su hadin kai ta hanyar bayar da bayani kan duk wasu ayyukan ‘yan bindiga da suka lura da su.

Kara karanta wannan

An kaddamar da shirin karban tuban 'yan bindiga da koya musu sana'o'i

Harin da dakarun sojoji suka kai kan ‘yan bindiga a dajin Sakkarawa wani babban ci gaba ne a yaki da ta’addanci a yankin Sabon Birni.

'Yan banga sun farmaki 'yan bindiga a Sokoto

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan banga sun kai mummunan farmaki kan 'yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar Katsina.

Rahotanni sun nuna cewa 'yan bangar sun kai farmakin ne da dare yayin da 'yan ta'addar suka sace wasu mutane a karamar hukumar Malumfashi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng