Gwamna Ya Kwaikwayi Abba Kabir na Kano, Ya Rabawa Mata Awaki 40,000
- Gwamna Malam Dikko Raɗɗa ya kaddamar da shirin rabon awaki ga mata da manoma domin bunƙasa harkokin kiwo a jihar Katsina
- Dikko Radda ya ce shirin wanda zai laƙume Naira biliyan 5.7 zai ba mata da manoma damar samun horo kan kiwon zamani da tallafi
- Gwamnatin Katsina ta tsara rabon awaki 40,000 a faɗin gundumomin Katsina tare da abincin dabbobi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina - Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya kaddamar da 'shirin kiwo' da rabon Awaki 40,000 da nufin mayar da jihar cibiyar noma da kiwo a Najeriya.
Gwamna Radda ya bayyana haka yayin da yake jawabi ga wadanda suka ci gajiyar shirin da shugabannin al’umma a karamar hukumar Daura ranar Litinin.

Asali: Facebook
Sakataren watsa labaran gwamnan, Ibrahim Kaula Muhammed ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Wannan mataki ne da zai kawo sauyi a fannin aikin noma da kiwo a jiharmu, kuma wata dama ce da za ta taimaka wajen bunkasa tattalin arziki da rage fatara," in ji Dikko.
Gwamna ya rabawa mata awaki
Shirin wanda ya laƙume Naira biliyan 5.7 zai bai wa mata da manoma damar samun horo da tallafi wanda zai taimaka masu wajen samun nasara a kiwo.
Gwamnan ya ce:
“Shirin zai bai wa mata damar dogaro da kansu ta hannun Ma’aikatar Harkokin Mata, kuma za a koya musu dabarun kiwon zamani da kula da lafiyar dabbobi.”
Yadda aka shirya rabon awakin a Katsina
An shirya rarraba awakin ga mutane da aka zaɓa ta hanyar kwamitin al’umma a gundumomi 361 na jihar Katsina.
Gwamna Radda ya ce:
“Mun tabbatar da cewa ba a yi son rai wajen zaben wadanda za su ci gajiyar shirin ba. A kowace mazaba, mata 10 za su amfana, kowacce mace za ta samu awaki hudu, namiji guda da mata uku.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba zai jiƙa mutanen Kano da ayyukan alheri, ya ware sama da Naira biliyan 30
"Babban makiyayi daya a kowace mazaba zai samu awaki 50. Za a biya bashin ne da da adadin dabbobin bayan wani lokaci.
Gwamnan ya bayyana cewa za a kafa sabuwar gona ta awaki a Rimi, domin samar da ingantattun awaki, madara, da taki.
"Za mu kafa wannan gona domin habaka kiwo da samar da dabbobi masu inganci ga manoma.”
Martanin sarakuna da shugabanni a Katsina
Kwamishinar harkokin mata, Hajiya Hadiza Yar’adua, ta yaba wa Gwamna Radda bisa yadda yake bai wa mata fifiko.
Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk, ya ce, “A cikin shekaru biyu kacal, Gwamna Radda ya ceto Katsina daga wahala zuwa ci gaba.”
Mai ba gwamna shawara kan harkokin kiwo, Hon. Yusuf Sulaiman Jibia, ya tabbatar da cewa an yi wa dabbobin rigakafi domin kare lafiyarsu.
Gwamnati za ta bai wa kowane mai cin gajiyar shirin abincin dabbobi da sinadaran kiwo don tabbatar da cewa shirin ya dore.
Ɗaya daga cikin matan da za su amfana da shirin tallafin, Binta Lawal ta shaidawa Legit Hausa cewa tabbas kiwo na ɗaya daga cikin sana'o'in da ke taimakawa mata.
A cewarsa, sana'ar kiwo musamman ta awaki da tumaki tana taimakawa mata da dama domin sun iya samar da abincin dabbobi daga aikace-aikacensu na gida.
"Ina daga cikin waɗanda aka zaɓa amma rabon bai kawo kanmu ba, an ce dai gwamna ya kaddamar a Daura. Ni dai dama ina kiwo kuma gaskiya muna samun alheri.
"Mun godiya ga gwamna kuma Allah ya taimake shi a waɗannan ayyukan taimako da yake yi, iya abinda zan ce kenan," in ji ta.
Gwamna Dikko ya rababwa matasa tallafi
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Dikko ya rabawa matasa da ƴan dabar siyasa tallafin Naira miliyan 252 a Katsina.
Malam Dikko Umaru Radda ya ce hakan na ɗaya daga cikin alƙawurran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zabe.
Asali: Legit.ng