An Yi Babban Rashi: Tsohon Ministan Najeriya Ya Rasu Yana da Shekaru 97

An Yi Babban Rashi: Tsohon Ministan Najeriya Ya Rasu Yana da Shekaru 97

  • Rahotanni sun ce tsohon ministan yaɗa labarai, kuma jagoran kungiyar 'yan Neja Delta, Edwin Clark, ya rasu yana da shekaru 97
  • Farfesa C. C. Clark, a madadin iyalan Edwin Clark ya fitar da sanarwar rasuwar jigon na Ijaw a daren Litinin, 17 ga Fabrairu, 2025
  • Rasuwarsa na zuwa ne kwanaki kadan bayan mutuwar jagoran Afenifere, Ayo Adebanjo, wanda ya rasu yana da shekaru 96

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Delta - Tsohon ministan yaɗa labarai na tarayya kuma jagoran yankin Kudu maso Kudu, Edwin Clark, ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayi Edwin Clark, wanda ya kasance shugaban ƙungiyar dattawan Neja Delta ta PANDEF, ya rasu yana da shekaru 97 a daren Litinin, 17 ga Fabrairu, 2025.

Iyalai sun sanar da rasuwar jagoran Neja Delta, Edwin Clark
Allah ya karbi rayuwar Edwin Clark, tsohon ministan Najeriya yana da shekaru 97. Hoto: @Mayor_ofph (X)
Asali: Facebook

Tsohon minista, Edwin Clark ya rasu

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa, labarin mutuwar Edwin Clark na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Farfesa C. C. Clark ya sanya wa hannu a madadin iyalansa.

Kara karanta wannan

Zamfara: Sojoji sun lalata sansanin rikakken dan ta'adda, sun kwashe buhunan abinci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sanarwar, Farfesa Clark ya bayyana cewa:

"Iyalan Clark-Fuludu Bekederemo na garin Kiagbodo, jihar Delta, suna sanar da rasuwar Cif (Dakta) Sanata Edwin Kiagbodo Clark, a ranar Litinin, 17 ga Fabrairu, 2025."

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

"Iyalan suna godiya da addu'o'inku a wannan lokaci. Za a sanar da cikakken bayani daga baya ta bakin iyalansa."

Rasuwar Edwin Clark ta biyo bayan mutuwar jagoran ƙungiyar Afenifere, Ayo Adebanjo, wanda ya rasu yana da shekaru 96.

Kadan daga tarihin rayuwar Edwin Clark

Wasu abubuwan sani masu muhimmanci game da rayuwar marigayi Edwin Clark
Wasu bayanai masu muhimmanci game da rayuwar marigayi Edwin Clark. Hoto: @Mayor_ofph (X)
Asali: Twitter

An haifi Edwin Kiagbodo Clark a ranar 25 ga Mayu, 1927, a garin Kiagbodo, jihar Delta, kamar yadda rahoton shafin WikiPedia ya nuna.

Ya kasance ɗan siyasa kuma jagoran al'ummar Ijaw, wanda ya taka rawar gani a harkokin siyasar Najeriya.

Clark ya fara karatunsa a Makarantar African Church a shekarar 1938, sannan ya halarci Kwalejin Koyon Malanta ta Gwamnati. Daga bisani, ya zama malami kafin ya tafi Birtaniya don samun digiri a fannin shari'a.

Kara karanta wannan

'Yan Shi'a fusata, sun ta aika kakkausan sako ga gwamnatin Tinubu

A fagen siyasa, Clark ya fara ne a shekarar 1953 lokacin da aka zaɓe shi a matsayin kansila na Bomadi, Delta.

Daga nan, ya yi aiki tare da gwamnatocin soja na Samuel Ogbemudia da Janar Yakubu Gowon tsakanin 1966 zuwa 1975.

A lokacin mulkinsa, ya riƙe mukamin kwamishinan bayani na tarayya a shekarar 1975. Hakanan, ya kasance mai ba da shawara ga tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.

Bayan ritayarsa daga aikin gwamnati, Clark ya kafa Jami'ar Edwin Clark a shekarar 2015, da ke garinsu Kiagbodo. Hakan ya nuna ƙudurinsa na inganta ilimi a yankinsa.

A matsayinsa na jagoran al'ummar Ijaw, ya kafa ƙungiyar PANDEF a shekarar 2016 tare da wasu shugabanni, domin tattaunawa da gwamnati kan ci gaban yankin Niger Delta.

Mutuwar Clark ta zo bayan rasuwar Adebanjo

Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa, jagoran Afenifere, Ayo Adebanjo ya rasu ne a safiyar Juma'a, 14 ga Fabrairu, 2025, a gidansa da ke Lekki, jihar Legas.

Ayo Adebanjo ya kasance sanannen lauya kuma ɗan gwagwarmayar siyasa, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen kafa ƙungiyar Afenifere don kare muradun Yarbawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel