Kungiyar PANDEF sun nuna jimami akan hatsarin Yusuf Buhari
- Kungiyar Pan Niger Delta Forum (PANDEF) sun taya uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari jimamin rauni da danta, Yusuf ya ji sakamakon hatsarin babur
- Hukumomin tsaro na gadin asibitin Cedar Crest inda dan shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jinya
Kungiyar Pan Niger Delta Forum (PANDEF) sunyi alhini da jimami kan hatsarin babur da ya cika da Yusuf Buhari.
A wata sanarwa da kungiyar ta PANDEF ta fitar sun taya uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, jimamin al’amarin, sannan sunyi addu’an Allah ya kara mata imani sannan ya ba Yusuf lafiya, jaridar Tribune ta ruwaito.
Kungiyar ta ce labarin ya zo mata a bazata sannan kuma sun kasa yarda.
KU KARANTA KUMA: Bazaku iya kayar da Buhari a 2019 ba – Tsohon kakakin PDP ga jam’iyyar adawa
A halin yanzu, rahoto daga jaridar Punch ya nuna cewa jami’an yan sanda da nay an sandan farin kaya na lura da asibitin Cedar Crest, yankin Gudu, Abuja inda dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf ke da kwanaki shida yana jinya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng