An Gano Dalilin Faduwar Farashi a Shahararriyar Kasuwar Abinci a Kano

An Gano Dalilin Faduwar Farashi a Shahararriyar Kasuwar Abinci a Kano

  • Farashin kayan abinci ya shafe akalla wata guda ya na sauka a fitacciyar kasuwar abinci ta Singer a jihar Kano
  • Shugaban kasuwar, Junaidu Zakari ya bayyana cewa shigo da kayan abinci daga kasashen ketare sun taka muhimmiyar rawa
  • Ana ganin farashin zai ci gaba da sauka ko ya kasance a yadda ya ke har zuwa azumi, ganin yadda abinci ya wadata a kasuwar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KanoBayanai daga manyan kasuwanni, musamman a jihar Kano, sun nuna saukin farashin shinkafa, wake, man girki, gero, da masara.

Shugaban kasuwar Singer, Junaidu Zakari, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Litinin, inda ya bayyana wasu daga cikin dalilan da suka jawo saukin.

Kara karanta wannan

Mutuwar mutane a hadarin Kano ya girgiza jama'a, Sanata Barau ya yi ta'aziyya

Getty
Farashin abinci ya sauka a kasuwar Kano Hoto: Getty
Asali: Getty Images

Jaridar Punch ta wallafa cewa cewa Shugaban ya danganta saukin da matakin da gwamnati ta dauka wanda ya ba ‘yan kasuwa damar shigo da wasu kayayyakin masarufi cikin sauki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce wasu daga cikin kayan da aka shigo da su sun hada da shinkafa, man girki, da taliyar leda, wanda hakan ya janyo raguwar farashin kayan abinci a Kano.

‘Yan kasuwa sun yabi manufar Tinubu

Junaidu Zakari ya ce ci gaban ya samu ne sakamakon matakin da gwamnatin tarayya ta dauka da kuma yadda ‘yan kasuwa da suka bi tsare-tsaren da aka shimfida.

Ya kara da cewa cire haraji kan wasu kaya guda 43 da kuma shigo da shinkafa da ake sayarwa kan N40,000 ya taimaka wajen wadatar kasuwanni da kayan abinci.

Yadda farashin abinci ya fadi a kasuwanni

Ya bayyana cewa shinkafa, wadda a baya ake sayar da ita kan N120,000, yanzu ta koma kasa da N80,000, yayin da taliya da aka sayar kan N20,000 yanzu ake sayar da shi kan N14,000.

Kara karanta wannan

Canada ya yi martani kan rahoton hana hafsan tsaron Najeriya shiga kasarta

Junaidu Zakari ya ce:

“Hakazalika, fulawa da aka sayar kan N90,000, yanzu ana sayar da ita a kasuwa kan kusan N70,000, yayin da man girki mai nauyin 50kg wanda a baya ya kai N100,000, yanzu ya koma N70,000,” in ji shi.

Sai dai ya ce har yanzu farashin sikari bai sauka ba, amma suna tattaunawa da kamfanonin Dangote da BUA domin ganin an rage farashin.

Zakari ya kuma zargi masu yin burodi da kin rage farashin, duk da cewa farashin fulawa ya ragu sosai a dukkan kasuwannin Kano.

Ramadan: Yadda farashi zai kasance a kasuwanni

Kwamred Bashir Mahmoud Madara, kakakin kasuwar Singer, ya tabbatar da cewa tun kusan wata daya da ya gabata farashin kayan abinci ke raguwa a kasuwar.

Ya danganta hakan da saukin samun kayan abinci daga gona, inda ya ce a baya kayan sun yi tsada ne sakamakon karancin kayayyakin noma daga yankunan karkara.

Kwamred Madara ya kara da cewa raguwar darajar Dala a kasuwa ya taka muhimmiyar rawa wajen rage farashin kayan abinci, kasancewar ana amfani da ita wajen shigo da kayayyaki.

Kara karanta wannan

Birkin tirela ya tsinke a Kano, ta murkushe mutane da dama

“Gaskiya ba ma fata kaya su motsa (da Azumi), don in za su motsa, a irin wannan lokaci suke motsawa—sati daya ko biyu kafin azumi, amma har yanzu ba su motsa ba.”

Ya ce idan har aka samu masu kara farashin kayan abinci saboda Ramadan, akwai alamun ba za su yi nasara ba, domin akwai wuraren da ake sayar da kayayyaki cikin sauki.

Gwamna ya karya farashin abinci

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Jihar Neja ta bayyana shirin samar da tallafi domin rage farashin kayan abinci yayin azumin watan Ramadan mai zuwa don saukaka wa jama'a.

Gwamna Umaru Bago ya shaida wa tawagar gidaniyar Bill Gayes cewa daya daga cikin manyan matakan da gwamnatinsa ke dauka domin tallafawa al’ummar jihar shi ne rage tsadar kayan abinci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.