Cikin Sarakuna Ya Ɗuri Ruwa, Gwamna Ya Yi Barazanar Tsige Su daga kan Sarauta

Cikin Sarakuna Ya Ɗuri Ruwa, Gwamna Ya Yi Barazanar Tsige Su daga kan Sarauta

  • Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benuwai ya yi barazanar tuge duk sarkin da aka gano yana bai wa miyagu mafaka a yankinsa
  • Alia ya ce ba zai yarda sarakun su ƙara dagula batun matsalar tsaro ba maimakon su ba da gudummuwa wajen tabbatar da zaman lafiya
  • Gwamna Alia ya yi wannan gargaɗi ne a wurin taron cika shekara guda da rasuwar sarki a Makurdi, babban birnin jihar Benuwai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Benue - Gwamnan Jihar Benue, Hyacinth Alia, ya gargadi sarakunan gargajiya a fadin jihar da su guji haɗa baki da miyagun da suka hana jama'a zaman lafiya.

Gwamna Alia ya jaddada cewa a shirye yake ya tube duk wani sarki da aka samu yana goyon bayan miyagu ko kuma yana basu mafaka a yankinsa.

Gwamna Alia.
Gwamna Alia ya yi barazanar tsige sarakunan da ke hada baki da miyagu a Benue Hoto: Hyacinth Alia
Asali: Twitter

Gwamna Alia ya ja kunnen sarakuna

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Gwamna ya bukaci jiragen yaki su rika sintiri a iyakokin Bauchi

Rahoton Vanguard ya tattaro cewa gwamnan ya bukaci sarakuna da su mayar da hankali wajen yaki da laifuka da rashin tsaron da ya addabi al'umma a yankunansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hyacinth Alia ya yi wannan jawabi a taron cika shekara guda da rasuwar Tor Sankera na farko, Marigayi Abu King Shuluwa, da nadin Elizabeth-Mary Shuluwa, wanda aka gudanar a gidan marigayi sarkin da ke Makurdi.

Ya bukaci shugabanni da masu ruwa da tsaki a Sankera da su fara shirin zaɓen sabon Tor Sankera, yana mai jaddada cewa dole sabon sarkin ya kasance mutum mai gaskiya, rikon amana, da kishin al’umma.

Alia bayyana cewa ya riga ya aika da buƙata ga Tor Tiv, Mai Martaba PFarfesa James Ayatse, don hanzarta zaben sabon Tor Sankera wanda zai kasance mai gaskiya da nagarta, domin ci gaba da inganta yankin.

Gwamnatin Benuwai na kokari kan tsaro

Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatinsa na aiki tukuru domin magance matsalolin tsaro da suka addabi Sankera, tare da dawo da zaman lafiya a yankin.

Kara karanta wannan

An kaddamar da shirin karban tuban 'yan bindiga da koya musu sana'o'i

Har ila yau, ya godewa limamin coci katolika da ke ƙaramar hukumar Katsina-Ala, Rabaraɓ Isaac Dugu, da kuma Tor Tiv, mai martaba Orchivirigh Prof. James Ayatse.

Alia ya godewa waɗannan manyan mutane biyu ne ebusa namijin kokarin da suke ci gaba da yi na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Gwamna Alia ya yi barazana ga sarakuna

A karshe, Gwamna Alia ya umarci dukkan sarakunan gargajiya da su tashi tsaye su ba da gudummuwa wajen yaki da miyagun laifuka a yankunansu da jihar baki ɗaya.

Ya kuma ƙara da jan kunnen kowane sarki cewa duk wanda aka samu yana goyon bayan ‘yan ta’adda, za a tube shi daga mukaminsa.

Gwamna ya kaddamar da taken Benue

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Alia ya ƙaddamar da taken jihar Benuwai da wasu alamomi domin bunkasa al'adu, asali da kuma tarihin jihar da ke Arewa ta Tsakiya.

Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta tabbatar da ci gaban jihar ta hanyar yakar koma-baya da gina ingantattun cibiyoyin lafiya da ilimi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262