Mutumin da Tinubu Ya Naɗa a Muƙami Ya Tsallake Rijiya da Baya, An Yi Yunƙurin Kashe Shi

Mutumin da Tinubu Ya Naɗa a Muƙami Ya Tsallake Rijiya da Baya, An Yi Yunƙurin Kashe Shi

  • Wasu miyagu sun farmaki babban daraktan ayyukan gine-gine na hukumar gidaje ta kasa watau FHA, Remi Omowaiye a jihar Osun
  • Omowaiye, wanda tsohon kwamishina ne ya faɗa tarkon maharan a lokacin da yake hanyar zuwa Osogbo yau Litinin, 17 ga watan Fabrairu, 2025
  • Ya ce miyagun sun buɗe wa motar da yake ciki wuta har sun fasa gilashin taga amma duk da haka ya samu ya tsira da ransa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun - Babban Daraktan Ayyukan Gine-gine na Hukumar Gidaje ta Tarayya (FHA), Remi Omowaiye, ya tsallake rijiya da baya a wani mummunan hari a jihar Osun.

Rahotanni sun nuna cewa mutumin wanda ke riƙe da muƙamin siyasa ya sha da kyar a harin, wanda wasu miyagu suka kai masa a kan titin Osogbo/Ilesa a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Fada ya barke tsakanin magoya bayan APC da PDP, an kashe mutum 2

Remi Omowaiye.
Babban darakta a hukumar FHA ya sha da kyar a harin kwantan bauna a jihar Osun Hoto: Remi Omowaiye
Asali: Facebook

Bisa bayanan da jaridar The Nation ta tattara, lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:05 na rana a gaban sakatariyar ƙaramar hukumar Ilesa ta Yamma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mahara sun buɗe wa mutumin wuta

Maharan sun buɗe wa Mista Omowaiye, tsohon kwamishinan ayyuka a Osun wuta a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Osogbo.

Majiyoyi sun bayyana cewa Omowaiye ya jagoranci wasu ƴan jam’iyyar APC zuwa hedikwatar ‘yan sanda a Ilesa domin neman kariya ga shugabannin kananan hukumomi da aka mayar.

Bayan sun bar ofishin ƴan sanda sun koma hedikwatar APC, kuma daga nan aka sallame kowa ya koma gida.

Yadda hadimin gwamnatin Tinubu ya tsira

Sai dai yayin da Omowaiye ya kama hanyar komawa Osogbo a cikin wata Toyota Hummer mai launin fari, maharan suka yi masa kwanton ɓauna.

An ce ya faɗa tarkon tsagerun ne a gaban sakateriyar ƙaramar hukumar Ilesa ta Yamma, inda aka farfasa motarsa da ruwan alburusai.

Kara karanta wannan

APC ta yi raddi ga Tambuwal, ta fadi dalilin raba garinsa da jam'iyyar

A wata hira da yayi da Punch bayan harin, Omowaiye ya bayyana cewa direbansa da wani ɗan sanda sun samu munanan raunuka.

Diraba da ɗan sanda sun samu raunuka

"Ina kan hanyar dawowa daga Ilesa zuwa Osogbo lokacin da muka ci karo da miyagun sun mana kwanton ɓauna. Sun buɗe wa inda nake zaune wuta, har alburusai suka fasa taga."
"Direbana da ɗan sandan da ke tare da mu sun sami munanan raunuka. An garzaya da su asibiti domin samun kulawa."

Har ila yau, Omowaiye ya bayyana cewa an kai wa motar sabon shugaban Ilesa ta Gabas hari a daidai wajen da aka yi masa kwanton ɓauna.

Ya yi kira ga hukumomi da su binciki lamarin tare da tabbatar da an hukunta waɗanda suka aikata wannan aika-aika.

An kashe ciyaman da wasu a Osun

Kuna da labarin cewa shugaban ƙaramar hukumar Irewale ya rasa ransa tare da wasu da dama da ciyamomin suka yi yunƙurin komWa ofis.

Hon. Abass ya jagoranci wasu shugabannin kananan hukumomi da aka sallama don karbe ofishin karamar hukumar bisa ga hukuncin kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262