Sanata Ya Ɗirkawar Jarumar Fim Ciki kuma Yana Shirin Aurenta? Bayanai Sun Fito

Sanata Ya Ɗirkawar Jarumar Fim Ciki kuma Yana Shirin Aurenta? Bayanai Sun Fito

  • Sanata Ned Nwoko (APC, Delta ta Arewa) ya musanta rahoton da ake yaɗawa cewa shi ne uban ɗan cikin da Jaruma Chika Ike ke ɗauke da shi
  • Nwoko ya kuma karyata cewa yana shirin auren jarumar masana'antar Nollywood, yana mai cewa labarin da ake yaɗawa ba gaskiya ba ne
  • Ya gargaɗi masu yaɗa jita-jitar da su dakata haka nan domin ba za su cimma burinsu na ɗauke masa hankali ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Delta - Sanata mai wakiltar Delta ta Arewa, Ned Nwoko, ya karyata rade-radin da ke cewa yana shirin auren fitacciyar jarumar masana'antar fim watau Nollywood, Chika Ike.

Sanatan wanda bai jima da sauya sheƙa daga PDP zuwa APC ba, ya musanta zargin cewa shi ya yi wa jarumar cikin da take ɗauke da shi yanzu haka.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima: "Arewa na fama da matsanancin talauci"

Chika Ike da Sanata Nwoko.
Sanata Ned Nwoko ya musanta jita-jitar cewa yana shirin auren jarumar Nollywood Hoto: @Prince_NedNwoko
Asali: Twitter

Ned Nwoko ya musanta raɗe-raɗin gaba ɗaya a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin Sanata Ned Nwoko kan jita-jitar

A wata sanarwar da ta fito daga ofishin daraktan hulɗa da jama’a na ofishin Sanata Nwoko, ya ce labarin da ake yadawa ba gaskiya ba ne.

"Mun samu labarin jita-jitar da ke cewa Sanata Prince Ned Munir Nwoko yana shirin auren Chika Ike a matsayin mata ta bakwai, kuma tana dauke da cikin shi.
"Wannan zance babu gaskiya a cikinsa, domin kuwa ba komai ba ne illa kage da jita-jita," in ji sanarwar.

Sanata y asa baki ka soyayar 2face?

Haka nan, Sanata Nwoko ya ce ba shi da wata alaka da batun soyayyar 2face Idibia da ‘yar majalisa, Natasha Osawuru.

"Haka kuma, labarin da ake yaɗawa cewa ya yi magana kan 2face da batun ƙarin aure duk ƙarya ne.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito da ake raɗe raɗin shugaban AfDB na shirin kawo wa Tinubu cikas a 2027

"A matsayinsa na mutum wanda ya shahara a duniya, yana da mata da ke cikin harkar fim, ba abin mamaki ba ne masu yada jita-jita su kirkiri irin wadannan labarai."

Matar sanatan ta goge shafinta na Instagram

A daidai wannan lokaci da wannna jita-jita ke cin kasuwa, matar Sanata Nwoko, Regina Daniels, ta goge shafinta na Instagram.

Lamarin da ya ƙara rura wutar rade-radin cewar akwai yiwuwar an samu saɓani a tsakanin ma'auratan.

Sanarwar ta kara da cewa a yanzu Sanata Nwoko ya maida hankali kan ayyukan da suka fi mahimmanci, kuma ba shi da lokacin da zai bata da irin wadannan rade-rade.

"Sanata Nwoko yana kan aiki a matakin kasa, yana kokarin cika alkawurran da ya dauka a siyasarsa, kuma ba shi da lokacin fadawa cikin abubuwan da za su ɗauke masa hankalin."

A karshe, ya gargadi masu yada jita-jita da ‘yan jarida su rika tabbatar da gaskiyar bayanai kafin su wallafa su, tare da jan hankalin jama’a da su yi watsi da wadannan rade-rade.

Kara karanta wannan

Ana zargin gwamna ya ɗirkawa fitacciyar jaruma ciki a Najeriya, gaskiya ta bayyana

Sanata Nwoko ya gargaɗi gwamnan Delta

A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata mai wakiltar mazaɓar Delta ta Arewa ya yi ikirarin cewa jam'iyyar APC ba ta buƙatar gwamnan jiharsa, Sheriff Oborevwori.

Bayan ya sauya sheƙa a hukumance, Sanata Nwoko ya buƙaci gwamnan ya yi zanansa a PDP domin jam'iyyar APC ba ta bukatar ya dawo cikinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel