An Kashe Shugaban Karamar Hukuma da Magoya Bayan APC, PDP Suka Kacame da Fada

An Kashe Shugaban Karamar Hukuma da Magoya Bayan APC, PDP Suka Kacame da Fada

  • Wasu da ake zargin 'yan bangar siyasar PDP ne sun kashe Mista Remi Abass, shugaban karamar hukumar Irewole da ke a jihar Osun
  • APC da PDP na jayayya kan iko da karamar hukumar, inda APC ta ce kotun daukaka kara ta dawo da shugabannin da aka sallama
  • An samu musayar harbin bindiga lokacin da 'yan bangar siyasar PDP suka kai hari ofishin, wanda ya haifar da mutuwar Abass nan take

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Osun - An kashe Mista Remi Abass, shugaban karamar hukumar Irewole, jihar Osun, bayan wasu da ake zargin 'yan bangar siyasar PDP ne suka mamaye sakatariyar Ikire.

Akwai sabani tsakanin APC da PDP kan ikon gudanar da gwamnatin karamar hukumar Irewole, tare da jayayya game da hukuncin kotu na makon jiya.

Kara karanta wannan

Fada ya barke tsakanin magoya bayan APC da PDP, an kashe mutum 2

Watra majiya ta fadi yadda aka kashe shugaban karamar hukuma a Osun
Osun: Wasu da ake zargin 'yan bangar siyasa ne sun kashe shugaban karamar hukuma. Hoto: @OfficialPDPNig, @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Osun: Ciyaman ya yi kokarin komawa ofis

APC na ikirarin cewa kotun daukaka kara ta dawo da ciyamomin da aka sallama, yayin da gwamnatin Osun ta ce an soke zaben, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A safiyar Litinin, Remi Abass ya jagoranci wasu shugabannin kananan hukumomi da aka sallama don karbe ofishin karamar hukumar bisa ga hukuncin kotu.

An ce da shigowarsu ofishin, wasu da ake zargin 'yan bangar siyasar PDP ne dauke da makami suka kai farmake su domin kwace ofishin daga hannun su.

Yadda aka kashe shugaban karamar hukuma

An rahoto cewa, an kashe shugaban karamar hukumar, Abbas, tare da raunata wasu mutane yayin da 'yan bangar siyasar suka fara harbi da bindiga.

Wata majiya ta bayyana cewa:

"Wasu mutane ne suka shiga harabar ofishin suna dauke da bindigogi, inda suka nufi kan shugaban. Sun kewaye shi, don haka bai samu damar tserewa ba, har suka kashe shi."

Kwamishinan harkokin gwamnati na jihar, Mista Soji Ajeigbe, ya bayyana cewa PDP ta rasa 'ya'yannsu biyu a hannun 'yan bangar siyasar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel