'Ba Ka Isa ba': APC Ta Nunawa Gwamnan Zamfara Yatsa da Ya Haramta Tarukan Siyasa
- Gwamnatin jihar Zamfara ta haramta duk wani nau'in taron siyasa, ciki har da gangami bayan rikicin da ya auku a garin Maru
- Yayin da gwamnatin ta ce matakin na wucin-gadi ne, ta kuma jaddada cewa ba ayi don a kun tatawa wani ko wata kungiya ba
- Sai da jam'iyyar APC ta ce ba za a hana ta gudanar da tarukanta na siyasa ba, don haka umarnin gwamnan ba zai yi tasiri kanta ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta hana dukkan tarukan siyasa a fadin jihar, ciki har da gangami ko jerin gwanon motoci, domin tabbatar da zaman lafiya.
Wannan matakin ya shafi dukkanin jam’iyyun siyasa kuma ya fara aiki nan take domin dakile rikice-rikicen da ka iya tasowa a jihar.

Asali: Twitter
Gwamnatin Zamfara ta hana tarukan siyasa
A wata hira da BBC Hausa, mataimaki na musamman ga gwamnan Zamfara kan harkokin watsa labarai, Mustapha Jafaru Kaura, ya bayyana dalilin matakin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mustapha Kaura ya ce rikicin siyasa da ya auku a karamar hukumar Maru da har ya jawo aka rasa rayuka tare da kona kadarori, ya tilasta gwamna daukar matakin.
Ya jaddada cewa gwamnati na cikin zaman makoki bisa wannan lamari, kuma an hana tarukan siyasa ne domin hana faruwar wani tashin hankalin.
'Ba a yi don tauye wani ba' Gwamnati
Hadimin gwamnan ya bayyana cewa haramcin ba zai kasance na dindindin ba, amma mataki ne na wucin-gadi don kaucewa kara dagula lamuran tsaro a jihar.
Gwamnatin Zamfara ta nanata cewa ba a dauki wannann mataki don tauye ‘yancin kowa ba, sai dai don tabbatar da zaman lafiya a jihar.
Mustapha Kaura ya kara da cewa jami’an tsaro sun samu umarni na daukar mataki kan duk wani mutum ko kungiya da ba za su bi wannan doka ba.
Sai dai jam’iyyar adawa ta APC a jihar ta soki wannan matakin, tana mai cewa mambobinta masu bin doka ne kuma ba sa tayar da fitina.
APC ta nunawa gwamnan Zamfara yatsa
Kakakin APC, Malam Yusuf Idris Gusau, ya ce babu wata doka ta kasa da ta hana tarukan siyasa, yana mai cewa wannan matakin abin dariya ne.
Ya ce gwamnatin Zamfara ta dauki wannan matakin ne bayan gangamin jam’iyyar APC da aka yi a ranar Asabar, wanda ya firgita su, inji rahoton Daily Trust.
Gusau ya ce jam’iyyar APC jam’iyya ce da aka tantance a matakin kasa, kuma gwamnati ba za ta hana su gudanar da harkokinsu ba.
Ya jaddada cewa mambobin jam’iyyar ba su saba doka, don haka za su ci gaba da taruka ba tare da tayar da hankalin jama’a ba.
Asali: Legit.ng