Rigima na Neman Ɓarkewa a Majalisa Kan Sabon Yunƙurin Tsige Kakakin Majalisa

Rigima na Neman Ɓarkewa a Majalisa Kan Sabon Yunƙurin Tsige Kakakin Majalisa

  • Zanga-zanga ta ɓarke a Majalisar dokokin jihar Legas kan raɗe-raɗin ana shirin sauke Hon. Majisola Meranda, mace ta farko daga matsayin kakaki
  • An ruwaito cewa ƴan Majalisa da ma'aikata sun nuna mata goyon baya a lokacin da ta isa zauren Majalisar tare da jami'an tsaronta
  • Majalisar Legas ta tsunduma cikin rikici ne bayan tsige Mudashiru Obasa daga matsayin kakaki, tare da naɗa Meranda a watan Janairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Zanga-zanga ta ɓarke a zauren Majalisar dokokin jihar Legas yau Litinin kan yunƙurin tsige sabuwar kakakin Majalisar, Hon. Mojisola Meranda.

Rahoto ya nuna cewa ƴan Majalisa da ma'aikata sun nuna rashin amincewa da yunƙurin, suna masu tabbatar da goyon bayansu da Meranda.

Meranda.
Ma'aikata sun ɓalle da zanga-zanga kan yunƙurin tsige Meranda daga matsayin kakakin majalisar dokokin jihar Legas Hoto: Hon. Mojisola Meranda
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce lamarin ya kara kamari bayan jami’an hukumar tsaro DSS sun mamaye majalisar da sanyin safiya, inda suka rufe ofisoshin Meranda, mataimakinta, da magatakarda.

Kara karanta wannan

DSS ta mamaye zauren majalisa, an rufe ofishin kakakin majalisa da mataimaki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da ya haddasa rigima a Majalisa

Tun bayan tsige tsohon Kakakin Majalisar, Hon. Mudashiru Obasa, a ranar 13 ga Janairu, 2025, rikici ya ɓalle a Majalisar wanda har yanzu aka gaza shawo kansa.

Ƴan Majalisa sun tuge Obasa ne bisa zargin cin hanci da rashawa, amma ya garzaya kotu domin kalubalantar matakin

Ma'aikatan Majalisa sun goyi bayan Meranda

Rahotanni sun nuna cewa lokacin da Meranda ta iso harabar majalisar da misalin karfe 11:15 na safe, ma’aikatan majalisa sun yi ta rera taken:

"Meranda Muke So! Meranda Muke So!"

Ma'aikatan sun nuna suna tare da mace ta farko da ta zama kakakin Majalisar dokokin Legas, kuma sun bayyana ɓacin ransu kan yunƙurin tsige ta.

A cikin zauren majalisar kuwa, jami’an DSS sun gwabza da ma’aikatan majalisar, inda suka yi kokarin hana su shiga.

A wani faifan bidiyo, an ga Meranda cikin ruɗani a yayin da jami'an tsaronta suka kewaye ta saboda yadda rigima ke neman kaure wa.

Kara karanta wannan

Shugaban Binance ya buɗe baki, ya jero sunayen ƴan Majalisa 3 da suka nemi cin hanci

APC ta rabu 2 kan tsige Obasa

Bayanai sun nuna cewa shugabannin APC a jihar Legas musamman majalisar GAC sun dare gida biyu kan tsige Obasa ɗa naɗa Meranda.

A cewar The Nation, an umurci ‘yan majalisar su nemi gafarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu saboda sun tsige Obasa ba tare da tuntuɓar shugabancin jam’iyya ba.

Haka kuma, wasu majiyoyi sun bayyana cewa Meranda na iya yin murabus yau Litinin domin ba wa Obasa damar komawa kan kujerarsa.

Ana sa ran kan ba da jimawa ba za a samu cikakken bsyani kan halin da ake ciki da kuma yiwuwar murabus din Hon. Meranda.

Dalilan tsige kakakin Majalisar Legas

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar dokokin jihar Legas ta bayyana muhimman dalilin da suka jawo tsige Hon. Mudashiru Obasa daga shugabanci.

Daga cikin manyan kura-kuran da da ake zarginsa tsohon shugaban majalisar da su har ta kai ga tsige shi sun haɗa da rashin zuwa taro da zaman majalisar a kan lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262